Aminiya

Baarcelona ta kori  Kocin matasa Baldes

Vicdtor Valdes

A ranar Lahadin da ta wuce kulob din FC Barcelona da ke Spain ya bayar da sanarwar korar kocin matasa na kulob din Bictor Baldes.

Baldes dai ya shafe kimanin shekara 14 yana yi wa Barcelona gola, bayan ya yi ritaya ne ya zama kocin matasa a watan Yulin bara.

ADVERTISEMENT

Tuni kulob din Barcelona ya tabbatar da sallamar Baldes a wata sanarwa da ya yi a shafin sadarwarsa.

Kafar watsa labarai ta Naija News ta kalato cewa Bictor Baldes ya samu matsala ce bayan ya samu sabani da Daraktan da ke kula da kulob din matasa na kulob din Patrick Kluibert da shi ma ya taba yi wa kulob din wasa a baya.

ADVERTISEMENT

An ce ya samu matsala ce a salon yin wasa da kuma yadda yake zabar ’yan wasa inda mahukunta kulob din suke ganin akwai son zuciya.