✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Baba Suwe ya sha alawashin daukaka kara game da soke hukunci

Fitaccen jarumin fina-finan harshen Yarabanci mai suna Baba Suwe ya ce zai shigar da kara a kotun koli don kalubalantar hukuncin da kotun daukaka kara…

Fitaccen jarumin fina-finan harshen Yarabanci mai suna Baba Suwe ya ce zai shigar da kara a kotun koli don kalubalantar hukuncin da kotun daukaka kara ta yi na hana hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) biyansa diyyar Naira miliyan 25.
Ya bayyana wa manema labarai ta bakin lauyansa, Mista Bamidele Aturu a karshen makon da ya gabata cewa za su daukaka kara zuwa kotun koli don tabbatar da cewa an yi adalci a shari’ar.
Ya ce: “Babu shakka za mu daukaka kara. Ai idan ba mu daukaka kara ba tarihi ba zai yafe mana ba saboda haka da zarar mun sami kofin hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke cikin kwanaki uku ko hudu da za mu shigar da kara a kotun koli.”
Ya ci gaba da cewa: “Idan kuka duba shaidun da hukumar ta dogara da su a doka ba su da amfani. Hukumar ta yi kuskuren yin amfani da sashe na 35 karamin sashe na (1) da karamin sashe na (c) na dokokin Najeriya domin dokar ba ta ba hukumar damar tsare Baba Suwe ko wani dan Najeriya ba, don kawai tana zarginsa da aikata laifi, ba tare da ta kai shi kotu ba.”
A ranar Juma’ar da ta gabata ne kotun daukaka kara da ke Legas ta soke hukuncin da mai shari’a Yetunde Idowu ta karamar kotu da ke Ikeja ta yi na ummartar hukumar NDLEA ta biya jarumin, wanda ake yi wa lakabi da Baba Suwe diyyar Naira miliyan 25 kan zarginsa da yunkurin safarar miyagun kwayoyi a 2011.
Alkalin kotun daukaka karar mai shari’a Rita Pemu ta bayyana diyyar miliyan 25 a matsayin marar amfani, sannan ta ce karamar kotun da ta yanke hukuncin ba ta da hurumin sauraren karar tauyen hakkin bil’adama da lauyan Baba Suwe ya shigar a ranar 24 watan Oktoban 2011.
Mai shari’ar ta bayyana cewa babbar kotun Gwamnatin Tarayya ce take da hurumin sauraren karar, musamman ma idan shari’a ta shafi laifukan da suka shafi kwayoyi. Saboda haka ta ce hukumar NDLEA tana da hurumin tsare wanda take zargi don yin bincike.