Da Dumi Dumi

Baba Suwe ya shigar da kara a kotun koli

Fitaccen jarumin nan da aka fi sani da Baba Suwe ya daukaka kara a kotun koli, yana kalubalantar hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na yin watsi da diyyar Naira miliyan 25 da babbar kotun Jihar Legas ta yanke wanda ya tilasta hukumar NDLEA ta ba shi sakamakon bata sunan da ta yi masa.
Lauyansa mai suna Bamidele Aturu shi ne ya shigar da karar a madadin jarumi Baba Suwe a ranar Juma’ar da ta gabata.
Lauyan ya nemi kotun kolin ta soke hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke, ta yi amfani da hukuncin da karamar kotu ta yanke wanda ya ummarci a biya shi diyyar Naira miliyan 25 tare da neman gafararsa.
Ita dai babbar kotun Jihar Legas ta ummarci hukumar NDLEA ta biya Baba Suwe diyyar Naira miliyan 25 a mtasayin bata sunan da ta yi masa lokacin da hukumar ta tsare shi tsawon kwanaki kan zargin hadiyar muggan kwayoyi amma kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin.
A takardar karar, Baba Suwe ya dage a kan cewa da kamata ya yi a ce kotun dauka karar ta tabbatar da hukuncin da babbar kotu ta yanke saboda hukumar NDLEA ba ta da hurumin tsare wani mutum na tsawon kwanaki ba tare da gurfanar da shi a gaban kotu ba kamar yadda sashe na 35 na kundin tsarin dokokin Najeriya ya tanada.
Ya musanta ikirarin da hukumar NDLEA ta yi na cewa tsare Baba Suwe da ta yi don ta bincike shi kan laifin da ake zargin ya aikata bai sabawa sashe na 35 ba.
Haka zalika ya yi watsi da hujjar da hukumar NDLEA ta bayar na cewa wani mutum da ta kama kwana uku bayan kama Baba Suwe ya kasayar da dauri 60 na miyagun kwayoyi a rana ta biyu da ta uku da kama shi.
“Duk wadannan ba hujjoji ba ne da za a dogara da su. Domin rashin kasayar da kwayoyin ba zai zama hujjar da kotun daukaka karar da za ta dogara da ita ba wajen zartar da cewa kwanakin 19 da hukumar ta tsare shi ba wani abu ba ne. Saboda haka hujjojin da kotun ta dogara da su ba wasu hujjoji ba ne za a ce an yi amfani da su wajen yin watsi da hukuncin da kotun farko ta yanke.” Inji shi.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya