✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babachir ya ziyarci fadar shugaban Najeriya

Tsohon sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya Babachir David Lawal ya ziyarci fadar shugaban kasa da ake Aso Villa Abuja. Tun bayan korar Babachir da aka yi…

Tsohon sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya Babachir David Lawal ya ziyarci fadar shugaban kasa da ake Aso Villa Abuja.

Tun bayan korar Babachir da aka yi a ranar 30 ga watan Oktoba 2017 kimanin watanni 13 da suka gabata, an kori tsohon Sakataren ne bayan samun sa da wasu badakalar kudaden kwangila wanda majalisar dattawa ta amince da dakatar da shi daga mukaminsa, Babachir ya ziyarci fadar shugaban Najeriya don halartar liyafar cin abinci da kungiyar magoya bayan tazarcen Shugaba Buhari wato Buhari Support Organization (BSO).