✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babangida ya jinjina wa Gwamnatin Wamakko

Tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya jinjina wa gwamnatin Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko kan cin gaban da yake kawowa a jihar da kasa…

Tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya jinjina wa gwamnatin Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko kan cin gaban da yake kawowa a jihar da kasa baki daya.
Janar Babangida ya bayyana haka ne a Sakkwato lokacin ziyarar da ya kai ta kwana biyu.
Ya ce gwamnatin Wamakko gwamnati ce mai kokarin kawo ci gaba saboda ayyukan da ya gani, kamar shirin samar da wutar lantarki na jihar wanda zai taimaka wa jihar ta zama cibiyar masana’antu a Arewa.
Janar Babangida ya ce gwamnatinsa ce ta fara aikin Asibitin Murtala, amma aka yi watsi da shi sai yanzu ne Wamakko ke kokarin cika kudirinsa na ganin asibiti ya zama gaskiya.
Shugaban a ziyararsa ya bude sabon gidan saukar Shugaban kasa da hanyoyi da wurin koyon kiwon kaji da sauransu.