Da Dumi Dumi

Babban abin da nake buri a rayuwa – Fatima Ali Sheriff

Fatima Ali Sheriff
Fatima Ali Sheriff

Malama Fatima Ali Sheriff fitacciya ce wajen koyar da sana’o’i ga mata da matasa a Jihar Borno, tun tana karama. Hakan ya sa ta samu lambobin yabo daga kungiyoyi, kuma ta kafa gidauniyar tallafa wa jama’a mai suna Zumzum Foundation. A zantawarta da Aminiya ta bayyana tarihin rayuwarta da kuma burinta:

Tarihina

Sunana Fatima Ali Sheriff, an haife ni a Unguwar Lawan Bukar a nan Maiduguri, kuma na girma a Unguwar Kasuwar Shanu. Na yi makarantar firamare a Gamboru 3 har zuwa sakandare duk a nan Maiduguri. Amma sai dai ina aji biyu a sakandare na bar makarantar boko, na koma Higher Islam, bayan na kammala na tafi Zariya, inda a can na ci gaba da karatu a wannan fanni. Ina Zariya mahaifiyata ta haihu, wanda sanin halin da take ciki na yanke karatuna na dawo gida domin in kula da ita. Don idan ban dawo na kula da ita ba za ta iya shiga cikin wani hali, a kan haka  karatuna a wancan makaranta ya yanke, har aka yi min aure.

Lokacin da aka yi min aure mijina bai bar ni na ci gaba da karatu ba. To amma da yake lokacin da aka yi min aure, dama na iya yin sakar rigar sanyi da karatun bai yiwu ba, sai na fara yin sakar ina bai wa kannena suna sayarwa. Idan wannan makon na ba wa daya, wani makon sai in ba wa wani, kuma ba na karbar kudin, nakan bar musu. Don su yi amfani wajen biyan bukatunsu, ganin mahaifinmu dan kwangila ne, wata rana akwai kudi, wata rana babu.

Tunda na yi aure na fara taimakon marasa galihu, domin akwai wani yaro, a unguwar da aka kai ni ina amarya, ka san idan amarya ta zo yara kan zo wasa gida. To akwai wani yaro da ba ya jin magana aka ce kada in yarda ya rika shiga gidana, domin yana da wani mugun hali.

ADVERTISEMENT

To sai na ga idan har aka bar shi a haka, kowa ya ki shi, zai iya zama babban mai laifi. Sai na ja shi a jiki, yana zuwa yana ayyukan gida, har ta kai na saka shi a makarantar boko, wanda a yanzu haka babban jami’an Kwastam ne. Kuma har gobe yana kula da ni, yana karfafa mini gwiwa wajen ci gaba da taimakon marayu da marasa galihu.

Kalubale

Gaskiya na gamu da kalubale sosai, don mun shiga cikin halin damuwa a rayuwa, amma duk da haka ban yi kasa a gwiwa ba, wajen tallafa wa jama’a. A haka nake zuwa koyon gyaran gashi a shagon wata mata da take kusa da gidan da muka koma. Domin halin da muka tsinci kanmu a ciki har ta kai da sai da muka sayar da gidan da muke ciki, inda wani abokin maigidana ya ba mu wani gida muka zauna.

To a nan ne na hadu da matar, na rika zuwa shagonta ina koyon aiki, har na gaya mata ina yin lalle a haka na fara samun masu son yin lalle a kullum, har na daina zuwa shagon. Sannu a hankali halin da muke ciki na kalubalen rayuwa ya fara tafiya.

  Fatima Ali Sheriff a tsakiya tare da wadansu mata da take koya musu sana’a
Fatima Ali Sheriff a tsakiya tare da wadansu mata da take koya musu sana’a

Sannan kalubale na biyu inda nake gudanar da cibiyata ta Zumzum Foundation don tallafawa da koyar da sana’a haya nake yi, domin ba ni da kudin da zan sayi wuri, don in samu damar ci gaba da taimaka wa al’umma.

Nasarori

Alhamdulillahi gaskiya sai godiya ga Allah,  domin a matsayina ta mace, na bada gudunmawa wajen bunkasa rayuwar

’yan uwana mata, kai har da maza wajen koya musu sana’ar da suke dogara da kansu. Kuma na samu lambar yabo dag kungiyoyi da dama, duk wannan nasara ce, sai godiya.

Burina

Burina shi ne in tabbatar da ganin na ci gaba kuma wannan cibiya ta fi haka, wajen tallafa wa jama’a musaman ’yan gudun hijira da marayu. Wanda kamar yadda na fada haka na ga mahaifiyata tana yi, kuma ni ma na tashi da yin haka. Kuma idan har mata za su koyi sana’a to gaskiya hakan zai taimaka wajen kara danko kauna da taimakon juna a tsakaninsu da mazansu.

A kullum idan ina horar da masu koyon aiki ko karantarwa nakan rika ba su shawara a kan koyon sana’a da kuma taimakon jama’a musamman marayu.

Sana’oi da nake koyarwa

Akwai sana’o’i da dama, kamar rini da dinki da saka da kiwo da lalle da kitso da kuma yin cincin wanda zuwa yanzu na yaye dalibai sama da 150. Kuma ba biyana ake yi ba, ina zabo marayu da ’yan gudun hijira da masu karamin karfi,ne kowa ya zabi sana’ar da yake so, in koya masa. Kamar yadda ka gani a kofa ga matasa nan na yin sana’o’i iri-iri.

Shawara ga matasa

To ina shawartar matasanmu da kada su raina sana’a komai kankantarta, domin ni, na fara da yin saka da kwarashi biyu ne. Amma yanzu sai hamdala, har ana dauka ta in koyar da kungiyoyi daban-daban, don haka kada mutum ya ce sai yana da babban jari zai fara yin sana’a.

Irin abincin da na fi so

Biskin hatsi da miyar kuka da kuma duk wani abinci na gargajiya.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya