✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babban Bankin Najeriya zai daina ba masu shigo da tufafi canjin kudi

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanya dokar daina ba masu shigo da dukan nau’o’in sutura canjin kudi da nufin bunkasa masakun cikin gida. Haka kuma…

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanya dokar daina ba masu shigo da dukan nau’o’in sutura canjin kudi da nufin bunkasa masakun cikin gida.

Haka kuma Babban Bankin ya amince da fitar da tallafin wasu kudade ga masu masakun na cikin gida domin gyara da bunkasa ayyukansu.

Wata sanarwar daga bankin ta ce, “Daga yanzu dukan masu canjin kudi dole su daina ba masu kasuwancin tufafi da kayayyakin da masaku suke samarwa canjin kudi,” kamar yadda Shugaban Bankin, Godwin Emifiele ya sanar.

Ya kara da cewa bankin zai dauki wasu matakai na hana masu safarar kayan ta barauniyar hanya domin bata shirin da bankin ke yi.

Emiefele ya bayyana cewa masakun Najeriya sun kai darajar Dala miliyan 10, kuma bangare ne da zai iya bayar da dimbin ayyukan yi ga mutane, wanda hakan ya sa bai kamata a yi watsi da su ba.

Kofar Masaqar Arewa da ke Kaduna

Sauran matakan da Babban Bankin ya dauki sun hada da “Bayar da tallafi ga masakun cikin gida domin shigo da auduga da za a yi amfani da su a masakun Najeriya, amma da alkawarin cewa masakun za su ci gaba da nemo kayayyakin a cikin gida Najeriya daga badi,” inji sanarwar.

Shugaban Bankin CBN ya ce shirin bankin na Anchors Borrowers zai fadada, inda za a fara bayar da tallafi na musamman ga masu noman auduga domin su samar da audugar da ake bukata wajen farfado da masaku. Sannan ya tabbatar da cewa za su taimaka sosai wajen samar da wutar lantarki a wasu bangarorin da masakun suke aiki.

Godwin Emifiele ya ce, tun a shekarar 2016 suka fara tattaunawa da gwamnonin jihohin Kano da Kaduna domin bukatar samar da tallafi ga masakun domin a san yadda za a samar da wutar lantarki a yankunan da suke.

 

Ba yau aka fara hana mu canji ba – Dillalan tufafi

Da suke magana game da wannan mataki na Babban Bankin Najeriya, dillalan tufafi a Kasuwar Kwari da ke Kano sun ce wannan ba wani sabon abu ba ne, domin a cewarsu dama can an hana shigo da tufafin a cikin kayayyaki 41 da Babban Bankin ya hana a rika bai wa canjin kudi.

Babban Jami’in Gudanarwa na El-Samad Tedtile, Alhaji Sammani Adamu ya ce dama can masu kasuwancin tufafi sun dade suna canjin kudinsu a wajen kananan masu canjin kudi ba a bankuna ba, “Wannan ba sabon abu ba ne a wajenmu domin tun lokacin da aka sanya tufafi a cikin kayayyaki 41 da za a daina ba canjin kudi, sai muka koma wajen ’yan kasuwar canji domin neman canjin kudade ba bankuna ba. Don haka mu a wajenmu tun wancan lokacin aka fara ba yanzu ba,” inji shi.

Wani dan kasuwar tufafi a Kasuwar Kwari, Alhaji Baballe Shugaba ya bayyana cewa tuntuni aka yi watsi da bangaren masaku, wanda hakan ya sa dole aka rufe da yawa daga cikin masakun da suke Najeriya. Ya ce masu masakun ne suka koma harkar shigo da kayan, sannan kuma aka hana musu canjin kudi. “Dama muna samun canjin kudi daga gwamnati ne? Ba ma samun wani tallafin canji tuntuni, don haka wannan matakin na Babban Bankin Najeriya bai da wani tasiri a gare mu, sai dai idan dama suna ba su canjin ne da sunanmu,” inji shi.

Wani dan kasuwar tufafi a Kasuwar Balogun a Jihar Legas, Abdulganiyyu Abdulkadar ya ce duk da cewa bai da masaniya a kan sabon matakin na Babban Bankin Najeriya, zai yi maraba da shi idan har an yi ne domin ci gaba kasar nan.