Search
Subscribe
Babbar jarrabawar da ta fi tsaya min a rai – Umaru Mutallab

Alhaji Umaru Abdul Mutallab

Babbar jarrabawar da ta fi tsaya min a rai – Umaru Mutallab

A makon jiya ne fitaccen attijirin nan dan kasuwa kuma tsohon Minista, Alhaji Umaru Abdul Mutallab ya cika shekara 80 a duniya. Aminiya ta zanta da shi kan rayuwarsa da sauran abubuwa da dama kamar haka:

 

Kana daga cikin wadanda miliyoyin ’yan Najeriya ke alfahari da su; yaya za ka bayyana yadda ka taso a Arewa a lokacin da akasarin jama’a ake kyamar ilimin boko?

Tasowa a Arewa a wancan lokacin abu ne mai ban sha’awa. Domin a wancan lokacin duniya na kwance lafiya kuma duk abin da kake so akwai shi, ciki kuwa har da ilimi.

An haife ni a Katsina amma daga baya muka koma Funtuwa da zama bayan da aka yi wa mahaifina canjin wajen aiki. A Funtuwa na shiga makarantar ta Elemantare wacce a wancan lokacin ake shekara hudu. Daga nan kuma za ka wuce makarantar gaba wato Midil inda za ka sake shekara uku. Sai muka shiga Kwalejin Gwamnati ta Zariya wacce yanzu ake kira da  Kwalejin Barewa ta Zariya. Mu ne dalibai na karshe da muka gama da tsohon tsarin  kwalejin wanda ake yi daga aji daya zuwa shida. A lokacin da muka yi karatu na hadu da mutane da dama daga wurare daban-daban na kasar nan kasancewa ana kawo dalibai ne daga jihohi 19 na Arewa don haka kusan kowace al’umma tana da wakilinta a makarantar. Wannan ya ba mu damar cudanya da juna da fahimtar al’adu da addinan junanmu.

Bayan mun kammala kuma na yi nasara, sai aka ba mu takardar gamawa, wacce ake kira Cambridge Certificate.  Na fara aiki a matsayin akawu a wani kamfanin kwararrun akantoci a Kaduna. Ana kiransa da PKF. Bayan na shafe shekara daya sai na wuce Kwalejin Harkokin Kasuwanci ta Achimota. Bayan mun shafe shekara daya sai Gwamnatin Najeriya ta Arewa ta ce duk mu zo mu tafi kasar Ingila don karo karatu saboda kasar Ghana tana da akidar gurguzu. Kuma marigayi Shugaban Ghana Kwame Nkruma yana da basira sosai. Shugaba ne mai son kawo canji a kasarsa da kasashen Afirka. Don haka muka je can muka yi shekara daya kafin mu dawo gida.

Ni da wadansu abokan karatuna  sai muka wuce Kwalejin South-West ta birnin Landan, muka sake yin shekara uku muka samu horo a kan aikin akanta muka gama. Ina daya daga cikin dalibai kalilan da suka gwammace su sake tsayawa a can su sake samun horo. Don haka sai na fara aiki da wani kamfani mai suna Fuller Jenks Beecroft da ke birnin Landan inda na yi musu aiki na wata 18 na samu gogewa a fannoni da dama kamar aikin akanta da aikin tara haraji da sauran sassan gudanarwa.

Daga can ne kuma aka dauke ni aiki a Kamfanin Kera Makamai na Najeriya (DICON), wanda reshe ne na Ma’aikatar Tsaro. Suka ba mu takardar daukar aiki muka fara aiki, na shugabanci sashen kudi. A wancan lokaci Kamfanin DICON an tsara shi ne don kera dukkan makaman da sojin Najeriya ke bukata. In za ku tuna an fara Yakin Basasa a lokacin. Don haka an sanya takunkumin sayar wa Najeriya makamai. Don haka sai muka fara kera wasu daga cikin makaman da aka yi wannan yaki da su.

Aiki a wannan ma’aikata ya bude mini ido a kan harkokin ayyukan soja, domin dole sai mun kare kasafinmu, Shugaban Ma’aikatar shi ne kuma Babban Sakataren Ma’aikatar Tsaro ta wancan lokacin. Na yi aiki da su na tsawon shekara uku daga bisani na koma Kamfanin Bunkasa Masana’antu na Arewa (NNDC) wanda an kafa shi da zimmar jawo masu zuba hannun jari.

Ka yi makarantar Islamiyya kamar sauran yaran Arewa?

Sosai ma na yi makarantar Islamiyya bayan elemantare.  Ban sha wahala ba, saboda a elemantare an koyar da mu ilimin addini kadan. Kuma da rana mukan je makarantu zaure, yayin da dare muke karaton allo irn wadda ake hura wuta.

Da yawa mutane suna tsammani za ka zama shaihin malami addini ne; shin kasancewar mahaifinka ma’aikacin gwamnati ne ya yi tasiri a kanka ka sauya zuwa  karatun boko?

Kwarai kuwa, mahaifina shi ne ya dage sai na yi karatun boko. Don haka shi ne ya ba ni kwarin gwiwa. Domin kamar yadda na fada da farko na yi nazarin addinin Musulunci da Larabci ne a makarantar Elemantare haka kuma na ci gaba. Na yi hadda wasu surori da dama na Kur’ani. A wancan lokaci ana koyar da addinin Musulunci da Larabci.

Ka cika shekara 80 a duniya amma har yanzu da karfinka, wadanne harkoki kake yi yanzu da suke debe maka kewa?

Gaskiya ne ya kamata a ce mutum yana wani abu da zai rika yi koyaushe saboda hakan zai taimaka wa lafiyarka. Duk da yake na bar aiki har yanzu akwai wasu harkokin da nake kula da su. Sai dai ba kamar a baya ba lokacin ina matashi da nake fara aiki daga 7:30 na safe, yanzu ina dan tabawa ne a sannu.

Ko kana motsa jiki a yanzu?

Lokacin da ina matashi ina yin wasanni. Na iya buga kwallon kafa sosai don ni ne ma Kyaftin din kungiyarmu. Kuma ina yin wasan kwallon bango (Fibes), amma na bari yanzu.  Kuma da ina yin wasan tsallake, amma yanzu abin da nake yi shi ne duk safiya idan na gama Sallah sai in sassarfa a gidana sau uku ko sau biyar da yake yana da girma. Idan rana ta fara fitowa sai in je in yi Sallar Walha in sake kwantawa.

Ka yi aiki da gwamnatocin soja biyu, yaya za ka bayyana  darussan da ka koya?

Janar Murtala mutum ne mai kula. Duk da yake ni ne Ministan Harkokin Tattalin Arziki da Ci Gaban Kasa, ya yi ta aikena zuwa kasashe da dama kan wasu ayyuka na musamman. A wancan lokaci Najeriya ta zama jigo wajen kafa Kungiyar Hada Kan Afirka (OAU). Mun fara ne a matsayin Kungiyar Nairobi daga nan sai ta Kasablanka kafin mu zama Kungiyar OAU. A lokacin Najeriya tana kokarin hada kan Afirka ne, an tura mu Addis Ababa don shiga tsakani. Marigayi Joe Garba ya yi kokari sosai a wancan lokaci. Don haka a lokacin da na gama aiki Obasanjo ya yi mini karramawar ban-kwana.

An sha fama sosai wajen kafa Bankin Jaiz, yaya lamarin ya gudana?

Bayan gama aiki da bankunan ’yan kasuwa, sai na ga ya dace in yi wa wannan sashe wani hobbasa. Ina daya daga cikin wadanda kasar Saudiyya ta gayyata don halartar taro kan tattalin arziki da Bankin Musulunci (IDB) ya hada. Na ga abubuwan da suka yi a can kuma irinsu ne nake son ganin na yi a nan.  Bayan na gama aiki da Bankin UBA sai na fara tunanin yadda zan kafa irin wancan banki wanda yake da tsari na musamman. Ba sa yin caca ko wani abu da ba ya kan tsari. Wata uku da suka gabata na je kasar Scotland inda na halarci wani taro kan yin ayyuka bisa tsarin halal, kuma ba an takaita taron  ga Musulmi ba ne kawai, a’a na duniya ne. Sannan Bankin Duniya ne ya dauki nauyin taron. Taron ya bada horo ne a tsarin banki na Musulunci wanda ya hana duk wani abu da ya saba wa shari’a. Kuma muna kokarin mu tabbatar ana bin ka’ida wajen aiwatar da aikin banki kuma komai na tafiya yadda ya kamata.

Yaya aka ka kauce wa yunkuri da dama na a ba ka sarautun gargajiya?

Mutane da dama sun yi ta samuna da wannan bukatar. Ko marigayi Sarkin Katsina, Alhaji Kabiru Usman ya taba neman ya ba ni sarauta, amma na ci gaba da cewa, ‘ba yanzu ba.’ Yakan kai ni kauyauka yana gwada mini in zabi inda nake so, amma sai in ce masa sai daga baya.

Ku uku kun kaurace wa siyasa. Shin ba a taba neman ka shiga cikinta ba ce?

Muna goya musu baya tare da karfafar gwiwarsu. Cikinmu ba wanda ya tsunduma a siyasar gadan-gadan. Sai dai mun taimaka musu, mun kuma yi ta ba su shawarwari tare dafa musu.

Kana ganin za a iya kawar da rikicin kabilanci da bambancin addini a Arewa?

Ina kallon batun kabilanci da yadda ke da tasiri gare mu. In kana kaunar samun ilimi to lallai ne a kanka ka yi watsi da wannan don ka cimma nasararka. Ya rage gare ka san yadda za ka yi domin cimma muradunka. Ka ga yanzu mutane na wasa da hankalin mutane ta fakewa da kabilanci da addini suna cewa: Ai saboda wane Musulmi ne ya sa aka ba shi mukami kaza. Bai kamata ya zama ana haka ba, saboda ai Allah guda muke bauta wa kuma Yana sane da wanda Ya fi bauta maSa yadda kamata. Ina ma a ce gwamnatocinmu a dukkan matakai za su dafa wa harkar ilimi a kowane mataki, yadda ya dace. Wannan ne kawai hanya guda da za mu iya fitar da kanmu daga wannan tunani na rashin daidaito.

Yaya kake ji idan mutane suka ce kana cikin manyan attajirai kuma masu fada-a-ji a Najeriya?

Ban san daga ina mutane suka samo wannan tunani ba. Ba na ganin haka a kaina. Na wadata da abin da Allah Ya hore mini. Godiyar Allah na daga cikin muhimman ababuwa a rayuwa. Kai ta ma fi dukiyar. Ba ni da fada-a-ji a siyasa. Ina ga kawai abin yana da nasaba ne da idan kana girmama mutane kuma kana kyautata musu to su ma za su saka maka da abin da ka yi musu.

Ko akwai wani lokaci a rayuwarka da za ka kwatanta a matsayin wanda ka hadu da babbar jarrabawa a rayuwa?

Zan ce al’amarin Malam Farouk ne (dana) ya zame mini babbar jarrabawar da ta yi min tsaye a rai. Ina ci gaba da yi masa addu’a. Mukan ziyarce shi, kuma lokaci zuwa lokaci yakan kira mu gaisa. Sai dai mu ba ma iya kiransa, sai in ya kira mu. Mun san cewa yana cikin mayuwacin halin rayuwa, don haka rokar masa afuwa a madadinsa. Insha Allah wata rana za mu gan shi ko a Kiyama, saboda an yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai har sau uku tare da wasu shekarun a kurkuku ba tare da damar a sallame shi ba …(dogon numfashi).

Da wuya ya fito daga kurkuku ya gan mu. Don haka ina za mu sake haduwa da shi a gobe Kiyama. Yana yi mana addu’a ma mu ma muna yi masa. Ta haka ne muke rayuwa da wannan al’amari. Allah ne Mafi sanin abin da ya dace. A lokacin da na ji batun, ban taba tunanin shi ne ba. Na yi tunani ko wani ne ya sace fasfonsa ya yi yunkurin aikata haka. Amma bayan kwana biyu sai na fahimci shi ne.

Mece ce shawararka ga shugabannin Najeriya?

Ina ga ya kamata su inganta al’amura a kasar nan. Sun yi kokari, amma dai ya kamata su kara zage dantse ta fuskar tsaro da makamashi da kuma ilimi. Ya kamata mu sanya muhimman bukatunmu inda suka dace. Duk kasar da ba ta da ilimi, to ta rasa madafa har abada. Ilimi kamata ya yi ya zama na kowa ne. Don haka ya kamata mu fitar da kudi mai yawa ga bangaren ilimi. Muna kiran kanmu da giwar Afirka ta fuskar tattalin arziki, amma karfin wutar lantarkinmu bai wuce megawat dubu shida ba. Wanda ko kadan bai kai karfin wutar lantarkin birnin Makkah ba. Makamashi shi ne komai, saboda idan babu shi ba za mu iya yin komai ba. Wannan zai taimaka mana ta fuskar habaka ilimi da bangaren noma da  sauransu. Wannan ita ce shawarata ga shugabannin Najeriya, lallai ne su yi aiki kan haka.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin