Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Babbar mota ta kashe mutum 15 a Kebbi

Wata babbar mota tirela dankare da kaya ta kashe mutum 15 masu yin sana’a a bakin hanya a garin Jega da ke Jihar Kebbi. Motar ta fito ne daga Legas a kan hanyarta ta zuwa Sakkwato.
Wani wanda abin ya faru a gabansa Bello M. Abubakar Jega ya shaida wa wakilinmu cewa a lokacin da direban ya shigo garin na Jega kusa da masu yin sana’ar lemu da biredi da dabino da sauran masu kananan sana’a a bakin hanya, sai kawai suka ga babbar mota ta kauce hanya ta yi cikin masu yin sana’o’in kafin kace kwabo nan take ta kashe mutum 15 inda aka kai mutum 48 a asibitin Jega domin ba su taimakon gaggawa.

ADVERTISEMENT