✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babi na Arba’in da Biyar: Gaggauta buda baki:

417. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Abu Hazim daga Sahli dan Sa’id cewa: “Lallai Manzon Allah…

417. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Abu Hazim daga Sahli dan Sa’id cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Al’ummata (mutane) ba za su gushe ba suna cikin alheri matukar suna gaggauta buda baki.”

418. An karbo daga Ahmad dan Yunus ya ce: “Abubakar ya ba mu labari daga Sulaiman daga dan Abu Aufa (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Na kasance tare da Annabi (SAW) sai ya yi azumi har sai da ya yini. Sai ya ce, ga wani mutum: “Sauka ka kwaba mini garin alkama da ruwa.” Sai (mutumin) ya ce, “Da dai ka saurara har ka cika yinin? Ya ce, “Sauka ka kwaba mini garin alkama da ruwa.” Idan ka ga dare ya fuskanci ta nan lallai mai azumi ya yi buda baki.”

Babi na Arba’in da Shida: Idan mutum ya yi buda baki a cikin Ramadan bisa zaton rana ta buya, sai ta bayyana ba ta buya ba, (shin zai biya wannan azumi?):

419. An karbo daga Abdullahi dan Abu Shaiba ya ce: “Abu Usama ya ba mu labari daga Hisham dan Urwa daga Fadima daga Asma’u ’yar Abubakar, (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Wata rana mun yi buda baki a zamanin Annabi (SAW) a lokacin yini mai gira-gizai, sa’an nan rana ta bullo.” Sai aka ce, wa Hisham: Shin an umarce su da biya? Ya ce, “Dole ne biya,” Ma’amar ya ce, “Na ji Hisham ya ce, “Ban sani ba shin sun biya ko kuwa a’a.”

Babi na Arba’in da Bakwai:

Azumin yara ya halatta. Umar (Allah Ya yarda da shi) ya ce ga wani mashayi a cikin Ramadan cewa: “Tir da kai! Yaranmu na azumi amma kai ba ka yi, sai ya yi masa bulalar haddi”:

420. An karbo daga Musaddad ya ce: “Bishiru dan Mufaddal ya ba mu labari daga Khalid dan Zakawan daga Rabi’ah ’yar Mu’awiz ta ce: “Annabi (SAW) ya aika a Ranar Ashura (10 ga watan Muharram) zuwa alkaryun Madina cewa: “Duk wanda ya waye gari na mai cin abinci, to, lallai ya cika sauran yininsa (da kamun baki). Wanda ya waye gari na azumi to ya ci gaba da azuminsa.” Ta ce, “Sai muka kasance muna azumtarsa a bayan haka, yaranmu ma na azumtarsa har mukan rika sanya musu kayan wasa na ulu. Idan dayansu ya yi kuka saboda abinci sai mu ba shi wannan abin wasa har lokacin buda baki.”

Babi na Arba’in da Takwas:

Zarcen azumi (wucewa da azumi har kwana uku, ko biyu babu buda baki tsakaninsu). Da maganar wanda ya ce, “Babu azumi a cikin dare bisa fahimtar maganar Allah Madaukaki cewa: “Ku cika azumin zuwa dare (2:187).” Annabi (SAW) ya hana yin zarce don jin kai gare su (Musulmi) da tsare lafiyarsu. Da bayanin hani game da zurfafawa a cikin addini wanda (Allah bai umurta da shi ba.):

421. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yahya ya ba mu labari ya ce, daga Shu’abah ya ce, “kattada ya ba ni labari daga Anas (Allah Ya yarda da shi) ya ce: Daga Annabi (SAW) ya ce, “Kada ku yi zarcen azumi.” Sai (sahabbai) suka ce, “Hakika kana zarce.” Ya ce, “Ba kamar ku nake ba, lallai ni ana ciyar da ni kuma ana shayar da ni, ko ya ce, ‘Ina kwana an ciyar da ni kuma an shayar da ni.”