Da Dumi Dumi

Babi na Biyar: Wanda ya kyamaci Madina:

Babi na Biyar: Wanda ya kyamaci Madina:
347. An karbo daga Abu Nu’aman ya ce, “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Sa’id dan Musayyib ya ce: “Lallai Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Za ku bar Madina a mafi alherin da ta kasance. Babu abin da ke lullube ta (zama cikinta) face tsuntsaye da shaho, yana nufin dabbobi masu cin nama da tsuntsaye. karshen wanda za a tayar da su su ne makiyaya biyu daga kabilar Muzaina za su yi nufin zuwa Madina sai su iske babu kowa cikinta lokacin da suka isa Kwarin Saniyyat sai su fadi bisa fuskokinsu su mace.”
348. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Hisham dan Urwat daga Babansa daga Abdullahi dan Zubair daga Sufiyan dan Abu Zuhair (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai shi ya ce, “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Za a ci Yaman sai wasu mutane su yi nufin kaura daga (Madina) sai su nemi iyalansu da wadanda suke musu biyayya da yin kaura zuwa (Yaman). (Annabi SAW ya ce,) alhali Madina ce tafi musu alheri da sun kasance suna da sani. Kuma za a ci Sham (Siriya) da yaki, sai wasu mutane su yi nufin kaura daga (Madina) sai su nemi iyalansu da wadanda suke musu biyayya da yin kaura zuwa (Siriya). Alhali Madina taf i musu alheri da sun kasance suna da sani. Kuma za a ci Iraki da yaki, sai wasu mutane su yi nufin kaura daga (Madina), sai su nemi iyalansu da wadanda suke musu da’a (biyayya) da yin kaura zuwa (Iraki) alhali Madina ce ta fi musu alheri da sun kasance suna da sani.”

 Babi na Shida: Imani yana tarowa zuwa ga Madina:
349. An karbo daga Ibrahim dan Munzir ya ce: “Anas dan Iyad ya ba mu labari, ya ce Ubaidullahi ya ba ni labari daga Khubaib dan Abdurrahman ya ce, daga Hafsu dan Asim daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Hakika imani zai taro zuwa Madina kamar yanda macijiya take tarowa zuwa dakinta.”

 Babi na Bakwai: Laifin wanda ya yi wa mutane Madina sharri da yaudara:
350. An karbo daga Husain dan Hurais ya ce: “Fadalu ya ba mu labari daga Ju’aid daga A’isha (RA) ta ce, “Na ji Sa’ad Allah Ya yarda da shi ya ce: “Na ji Annabi (SAW) yana cewa, “Babu wanda zai yi wa mutane Madina yaudara da sharri face (Allah) Ya narkar da shi kamar yadda gishiri ke narkewa a cikin ruwa.”

Babi na Takwas: Manyan benayen (karkara) Madina:
351. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, dan Shihab ya ba mu labari ya ce, Urwata ya ba ni labari ya ce, “Na ji Usamata (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Annabi (SAW) ya taba hangen manyan benayen Madina sai ya ce: “Shin kuna ganin abin da nake gani? Lallai ni, ina ganin mafadar (alamun digo-digon) fitina a tsakanin gidajenku kamar wurin saukar ruwan sama.” Ma’amar ya karbo shi da Sulaiman dan Kasir daga Zuhuri.

ADVERTISEMENT

 Babi na Tara: Dujal ba ya shiga garin Madina:
352. An karbo daga Abdul’aziz dan Abdullahi ya ce: “Ibrahim dan Sa’ad ya ba ni labari daga babansa daga kakansa daga Abu Bakarat (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Ta’addancin Masihud Dujal ba ya shiga garin Madina. Domin zai iske ta tana da kofofi bakwai, a bisa kowace kofa da mala’iku biyu (masu tsaro).”

Share