Da Dumi Dumi

Babi na Goma Sha daya: Da fadar Annabi (SAW) cewa:

Babi na Goma Sha daya: Da fadar Annabi (SAW) cewa: Idan kun ga jinjirin wata ku yi azumi, idan kun ga shi ku ci.” Saliyata ya ce daga Ammar cewa: “Wanda ya yi azumin a yinin shakka, hakika ya saba wa Abu kasim (SAW).”
379. An karbo daga Abdullahi dan Maslamta ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ambaci Ramadan sai ya ce, “Kada ku yi azumi har sai kun ga jinijrin wata, kuma kada ku ci har sai kun gan shi. Idan an lullube wata ga barinku ku kaddara masa (kwanakinsa).”
380. An karbo daga Abdullahi dan Maslmata ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Abdullahi dan Dinar daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Wata dare ashirin da tara ne, kada ku yi azumi sai kun gan shi. Idan an rufe muku wata, to ku cika (Sha’aban) talatin.”
381. An karbo daga Abul Walid ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari daga Jabalata dan Suhaim ya ce: Na ji dan Umar (Allah Ya yarda da su), yana cewa: “Annabi (SAW) ya ce, “Wata kamar haka da haka yake, a na uku ya nade babbar yatsa (ya nuna wa mutane yatsun hannunsa biyu sau biyu amma na uku ya nade babbar yatsa, yana nufin ashirin da tara).”
382. An karbo daga Adamu ya ce: ‘Shu’abah ya ba mu labari ya ce, Muhammad dan Ziyad ya ba mu labari ya ce, “Na ji Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: “Annabi (SAW) ya ce, ko ya ce, “Abul kasim (SAW) ya ce, “Ku yi azumi domin ganinsa (wata) ku ci saboda ganinsa. Idan an rufe muku ganin wata ku cika watan Sha’aban kwana talatin.”
383. An karbo daga Abu Asim ya ce: “Daga dan Juraij daga Yahya dan Abdullahi dan Saifi daga Ikramata dan Abdurrahman daga Ummu Salma (Allah Ya yarda da ita), cewa: Lallai Annabi (SAW) ya yi wa matansa rantsuwar rashin shiga gare su har wata daya. Lokacin da kwana ashirin da tara ya shude sai ya tafi ga matansa sai aka ce masa: “Lallai kai, ka yi rantsuwa ba za ka shigo ba har wata daya.” Sai ya ce, “Lallai wata yana kasancewa ne daga yini ashrin da tara.”
384. An karbo daga Abdul’aziz dan Abdullahi ya ce: “Sulaiman dan Bilal ya ba mu labari daga Humaid daga Anas (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) ya yi wa matansa Ila’i (rantsuwar rashin shiga gare su), lokacin da kafarsa ta yi rauni. Sai ya zauna a Mashrub (bene) dare ashirin da tara, sa’an nan ya sauko (komo gida) sai suka ce: “Ya Manzon Allah! Ka yi rantsuwar wata za ka yi. Ya ce, “Hakika wata na kasancewa ashairin da tara.”

Share