Da Dumi Dumi

Babi na Goma Sha daya: Kamar abin da ya gabata

358. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Wahab dan Jarir ya ba mu labari ya ce, Babana ya ba ni labari ya ce: “Na ji Yunus ya ce daga dan Shihab daga Anas (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Ya Allah! Ka sayanya albarkar Madina sau biyu kamar yadda ka sanya wa Makka.” Usman dan Umar ya karbo shi daga Yunus.
359. An karbo daga kutaiba ya ce: “Isma’il dan Ja’afar ya ba mu labari daga Humaid daga Anas (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya kasance idan ya komo daga tafiya idan ya fara hangen benayen (katangun) Madina. Sai ya kara sauri da taguwarsa, idan yana kan wata dabba ce, sai ya kara zaburar da ita, saboda nuna son Madina.”

 Babi na Goma Sha Biyu: Annabi (SAW) ya ki a bar Madina ba kowa
360. An karbo daga dan Sallam ya ce: “Alfazari ya ba mu labari daga Humaid dawili daga Anas (Allah Ya yarda da shi), ya ce: ‘Wata rana kabilar Bani Salmat sun yi nufin su kauro zuwa kusa da Masallaci. Sai Manzon Allah (SAW) ya ki a bar wani fili a Madina ba kowa, sai ya ce: “Ya kabilar Bani Salmat shin ba ku son a lissafa (saka) muku ladar zambiyarku (tafiyarku) ne? Sai suka zauna can ba su yi kaurar ba.”

 Babi na Goma Sha Uku: Abin da (Annabi) ya ce, game da Raudah
361. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yahya ya ba mu labari daga Abdullahi dan Umar ya ce, Khubaib dan Abdurrahman daga Hafsu dan Asim daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Abin da ke tsakanin dakina da mumbarina dausayi ne daga dausayin Aljanna, kuma mumbarina yana a bisa tafkina ne.”

362. An karbo daga Ubaid dan Isma’il ya ce: “Abu Usamata ya ba mu labari daga Hisham daga Babansa daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Lokacin da Manzon Allah (SAW) ya iso Madina, sai Abubakar da Bilal suka fara rashin lafiya. Kuma shi Abubakar ya kasance idan wata cuta (zazzabi) mai tsanani ta kama shi, yakan rika cewa a wake: “Kowane mutum mai waye gari ne a cikin iyalansa, alhali mutuwa tafi kusa da shi a kan igiyar dangarafansa (takalmar kafansa).” Bilal kuma shi ma idan zazzabin ya kama shi da zafi yakan rika cewa: “Kaicon wakata, kodai zan kwana a wannan dare ne a tsakanin ciyawar tsaure da jalil (ciyawa ce mai kamshi). Shin ko zan sha daga ruwan Majanat, ko kuwa tsaunukan Shama da dafil za su bayyana mini kuwa.” Sai Annabi (SAW) ya ce, “Ya Allah! Ka la’anci Shaiba dan Rabi’at da Utba dan Rabi’at da Umayyat dan Khalf kamar yadda suka fitar da mu daga kasarmu zuwa kasa mai annoba. Sa’an nan Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ya Allah! Ka sanya mana son Madina kamar yadda muke son Makka, ko ya fi haka. Ya Allah! Ka sanya albarka a cikin awon sa’inmu da mudunmu. Ka inganta (ba mu) lafiya, ka cire annobarta (Madina) zuwa Juhfah.” A’isha ta ce, “Mun isa Madina lokacin da take mafificiyar annobar kasar da Allah Ya halitta. Ta ce, “Kwarin Badhan ya kasance na gudanar da gurbataccen ruwan sha,” tana nufin ruwa mara tsabta.

ADVERTISEMENT

363. An karbo daga Yahya dan Bukair ya ce, “Laisu ya ba mu labari daga Khalid dan Yazid daga Sa’id dan Abu Bilal ya ce, daga Zaid dan Aslam ya ce, daga Babansa daga Umar (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Ya Allah! Ka azurta ni da mutuwar shahada a tafarkinKa, kuma Ka sanya mutuwata a garin ManzonKa (SAW).”

Share