Da Dumi Dumi

Babi na Goma Sha Shida: Bisa fadar Allah Madaukaki cewa:

Babi na Goma Sha Shida:

Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ku ci ku sha har sai farin zare (hasken alfijiri) ya bayyana muku daga bakin zare (duhun dare) na alfijiri. Sa’an nan ku cika azumin zuwa dare…(k:2:187).” Barra’u ya karbo daga Annabi (S.A.W).”
389. An karbo daga Hajjaju dan Minhal ya ce: “Hushaim ya ba mu labari ya ce, Husain ya ba mu labari ya ce, Husain dan Abdurrahman ya ba mu labari daga Sha’abi daga Addiyi dan Hatim (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Lokacin da wannan aya ta sauka cewa: “Ku ci ku sha har sai farin zare (hasken alfijiri) ya bayyana muku daga bakin zare (duhun dare)…, sai na dauki bakin zare da kullin farin farin zare na sanya su karkashin matashina. Na rika dubawa a cikin dare babu abin da ya bayyana mini, sai na tafi zuwa ga Manzon Allah (SAW) na ba shi labarin haka, sai ya ce: “Abin da ake nufi duhun dare da hasken yini.”

390. An karbo daga Sa’id dan Abu Maryam ya ce: “dan Abu Hazim ya ba mu labari daga Babansa daga Sahlu dan Sa’ad Hawwala Sanad ya ce, Sa’id dan Abu Maryam ya ba ni labari ya ce, Abu Ghassan Muhammad dan Mudarraf ya ba mu labari, ya ce, “Abu Hazim ya ba ni labari daga Sahlu dan Sa’ad ya ce: “An saukar da wannan aya cewa: “Ku ci ku sha har sai farin zare (haske fajiri) ya bayyana muku daga bakin zare (duhun dare), bai saukar da cewa: Daga alfijiri ba, sai mutane suka kasance idan suna azumi sai dayansu ya rika daura farin zare da bakin zare a kafarsa. Bai gushewa na cin abinci har sai ganinsu ya bayyana masa. Sai Allah Ya saukar da cewa: Daga Alfijiri – sai suka san cewa, lallai Shi Yana nufin dare da yini.”

Babi na Goma Sha Bakwai:
Da maganar Annabi (SAW) cewa: “Kada Kiran Sallar Bilal ya hana muku cin abinci lokacin sahur:
391. An karbo daga Ubaid dan Isma’il ya ce: “Daga Usamata daga Ubaidullahi daga Nafi’u daga dan Umar (Allah Ya yarda da su) da Alkasim dan Muhammad daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), cewa: “Lallai Bilal ya kasance yana kiran Sallah ne da dare. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ku ci ku sha har dan Ummu Maktum ya kira Sallah, domin lallai shi ba ya kiran Sallah sai alfijiri ya bullo.” Alkasim ya ce, “Babu abin da ke a tsakanin kiran sallarsu face kamar in wannan ya hau, sai wannan ya sauka.”

ADVERTISEMENT

Babi na Goma Sha Takwas: Gaggauta sahur (cin abinci kafin fitar alfijiri):
392. An karbo daga Muhammad dan Ubaidullahi ya ce: “Abdul’aziz dan Abu Hazim ya ba mu labari daga Abu Hazim daga Sahlu dan Sa’ad (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Na kasance ina yin sahur a wurin iyalaina, sa’an nan saurina yakan kasance domin in riski sahur (Sallar Asuba) tare da Manzon Allah (SAW).”      

Share