Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Babi na Goma sha Uku:

Abin da aka hana mai Ihrami namiji ko mace game da turare. A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Mace mai Ihrami ba za ta daura tufafin da turaren Waras ko Zafaran ya shafa.”           
   
313. An karbo daga Abdullahi dan Zaid ya ce: “Laisu ya ba mu labari, ya ce, Nafi’u ya ba mu labari daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Wani mutum ya mike sai ya ce, Ya Manzon Allah! Me za ka umarce mu da daurawa na tufafi a cikin Ihrami? Sai Annabi (SAW) ya ce, “Kada ku daura taguwoyi (riguna) ko wanduna, ko rawunna, ko alkyabbu face ga dayanku wanda bai samu dangarafi ba (takalma mara sa rufi), sai ya daura Khuffi biyu ya yanke karkashin Khuffin daga idon sawu (kafa). Kuma kada ku daura tufafi da wani abu na turaren Zafaran ko Warasu ya shafa. Kuma kada mace mai Ihrami ta rufe fuskarta kuma kada ta sanya safar hannu.”
314. An karbo daga kutaiba ya ce: “Jarir ya ba mu labari daga Mansur daga Alhakam daga Sa’id dan Jubair daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Wata taguma ta kayar da wani mutum ta taka shi ta kashe shi. Sai aka zo da shi ga Manzon Allah (SAW) sai ya ce: “Ku wanke shi, ku yi masa likkafani, amma kada ku rufe kansa, kuma kada ku sanya masa turare domin lallai shi za a tashe yana mai Ihrami (da Hajji).”

ADVERTISEMENT

 Babi na Goma Sha Hudu:
Wanka ga mamaci mai Ihrami da aikin Hajji. dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Mai Ihrami yana shiga dakin wanka.” dan Umar da A’isha ba su ga laifin susa ba ga mai Ihrami.”

 315. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Zaid dan Aslam daga Ibrahim dan Abdullahi dan Hunain daga Babansa cewa: Lallai Abdullahi dan Abbas da Miswar dan Makhramat sun yi sabani a Abwa’u. Sai Abdullahi dan Abbas ya ce, “Mai ihrami zai iya wanke kansa. Miswar ya ce, “Mai Ihrami ba zai wanke kansa ba,” sai Abdullahi dan Abbas ya aike ni zuwa ga Abu Ayyubal Ansari sai na iske shi na wanka a tsakanin manyan tukwanen (akusan) itace biyu ya lulluba (shamaki) da tufafi sai na yi masa sallama. Ya ce, “Wane ne wannan? Na ce, “Abdullahi dan Hunain ne, Abdullahi dan Abbas ya aiko ni gare ka in tambaye ka game da yadda Manzon Allah (SAW) yake wanke kansa lokacin da ke Ihrami? Sai Abu Ayyubal Ansari ya sanya hannunsa bisa tufafi ya lankwasa (bude) kansa har ya nuna min kansa. Sa’an nan ya ce, “Mutum yakan zuba a kansa, zuba sai ya zuba a kansa, sa’an nan ya goge kansa da hannayensa, ya yi baya da su ya komo. Ya ce, “Kamar haka na ga (SAW) yake aikatawa.”

ADVERTISEMENT

 Babi na Goma Sha Biyar:

daura takalman Khuffi ga wanda bai samu dangarafai (takalma marasa rufi) ba
316. An karbo daga Abul Walid ya ce: “Shu’aba ya ba mu labari, ya ce, Amru dan Dinar ya ba ni labari, ya ce: “Na ji Jabir dan Zaid ya ce, na ji dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Na ji Annabi (SAW) yana huduba a Arfa da cewa: “Wanda bai samu dangrafai (takalmi mara rufi) ba, to, yana iya daura Khuffi biyu. Wanda bai samu gyauto ba, to ya daura (sanya) wando alhali yana mai Ihrami.”