✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babi na Hudu: kofar Rayyan ga masu yin Azumi kadai

Babi na Hudu: kofar Rayyan ga masu yin Azumi kadai 369. An karbo daga Khalid dan Makhlad ya ce: “Sulaiman dan Bilal ya ba mu…

Babi na Hudu: kofar Rayyan ga masu yin Azumi kadai

369. An karbo daga Khalid dan Makhlad ya ce: “Sulaiman dan Bilal ya ba mu labari ya ce, Abu Hazim ya ba ni labari daga Sahlu (Allah Ya yarda da shi), daga Annabi (SAW) ya ce: “Lallai a cikin Aljanna akwai wata kofa wadda ake kiranta da suna Rayyan, masu yin Azumi kadai suke shiga daga gare ta Ranar kiyama. Babu wani daban wanda zai shige ta daga waninsu. Za a rika cewa: Ina masu yin Azumi? Sai su mike babu wani mai shiga ban da su, idan sun shiga sai a rufe (kulle) babu wani mai shiga.”
370. An karbo daga Ibrahim dan Munzir ya ce: “Ma’anu ya ba mu labari, ya ce, Malik ya ba mu labari daga dan Shihab daga Humaid dan Abdurrahman daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Wanda ya ciyar da abubuwa biyu domin Allah za a kira shi daga kofofin Aljanna cewa: Ya bawan Allah! Wannan alherinka ne. Wanda ya kasance daga cikin masu yawaita Sallah, za a kira shi daga kofar masu Sallah. Wanda ya kasance daga masu jihadi za a kira shi daga kofar masu jihadi. Wanda ya kasance daga masu yawaita azumi za a kira shi daga kofar Rayyan. Wanda ya kasance daga masu yawaita sadaka za a kira shi daga kofar masu yin sadaka.” Sai Abubakar (Allah Ya yarda da shi) ya ce, “Babana da Uwata fansa ne gare ka: Shin akwai wanda za a kira shi daga dukkan kofofin nan? Ya ce, “Na’am, ina kaunar ka kasance daga cikinsu.”
Babi na Biyar:
Shin za a iya cewa: Ramadan ko watan Ramadan? Da bayanin cewa, akwai wanda ke ganin haka duk daya ne. Annabi (SAW) ya ce, “Wanda ya yi azumin Ramadan.” Kuma ya ce, “Kada ku gabaci Ramadan da azumi.”
\371. An karbo daga kutaiba ya ce: “Isma’il dan Ja’afar ya ba mu labari daga Abu Suhail daga Babansa daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Idan watan Ramadan ya shigo sai a bude kofofin Aljanna.”
372. An karbo daga Yahya dan Bukair ya ce: “Laisu ya ba ni labari daga Ukailu daga dan Shihab ya ce, “dan Abu Anas bawan Taimiyyin ya ba ni labari cewa: “Lallai Babansa ya ba shi labari cewa, lallai shi ya ji Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Idan watan Ramadan ya shigo sai a bude kofofin Aljanna, a kulle (rufe) kofofin Jahannama, a daure shaidanu a cikin sarka.”
373. An karbo daga Yahya dan Bukair ya ce: “Laisu ya ba ni labari daga Ukail daga dan Shihab ya ce, Salim ya ba ni labari cewa: Lallai dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Idan kun gan shi (jinjirin watan Ramadan) ku yi azumi. Idan kun gan shi (jinjirin watan Shawwal) kuma ku ci, idan an rufe muku (jinjirin watan) ku kaddara masa (kwanakinsa).” Wani ya ce, daga Laisu ya ce, Ukail ya ba ni labari da Yunus cewa: Idan kun ga jinjirin watan Ramadan.”