✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babi na Shida: Wanda ya yi azumin Ramadan bisa imani da kyawon niyya

Babi na Shida: Wanda ya yi azumin Ramadan bisa imani da kyawon niyya. A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: Daga Annabi (SAW) cewa:…

Babi na Shida:

Wanda ya yi azumin Ramadan bisa imani da kyawon niyya. A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: Daga Annabi (SAW) cewa: “Mutane za a ta she su ne (kuma a yi musu sakayya) a bisa kyawon niyyarsu.”
374. An karbo daga Muslim dan Ibrahim ya ce: “Hisham ya ba mu labari ya ce, Yahya ya ba mu labari daga Abu Salmata daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), daga Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya tsayu (ya yi aikin nafila) a Daren Lailatul kadari bisa imani da neman lada za a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa. Wanda ya yi azumin Ramadan bisa imani da neman lada za a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa.”

Babi na Bakwai: Lokacin da Annabi (SAW) ya fi alheri ciki, idan Ramadan ya kasance:
375. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Ibrahim dan Sa’ad ya ba mu labari ya ce, dan Shihab ya ba mu labari daga Ubaidullahi dan Abdullahi dan Utbah cewa: “Lallai dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Annabi (S.A.W) ya kasance mafi alherin mutane. Kuma yakan fi alheri idan aka ce Ramadan ya kasance lokacin da yake haduwa da Jibrilu, saboda Jibrilu (AS) ya kasance yana zuwa masa a kowane dare a cikin Ramadan har kashen wata. Annabi (SAW) ya kasance yana karatun Alkur’ani daga gare shi. Idan Jibrilu ya hadu da shi yakan kasance mafi alheri daga iska mai kawo hadarin ruwa.”

Babi na Takwas: Wanda bai bar shaidar zur (karya) da aiki da ita a cikin Azumi ba:
376. An karbo daga Adamu dan Abu Iyas ya ce: “dan Abu Zi’ib ya ba mu labari ya ce, Sa’id Makburi ya ba mu labari daga Babansa daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) ya ce, “Wanda bai bar maganar zur da aiki da shi ba. To Allah ba Ya da wata bukata ga barin cin abincinsa ko abin shansa.”

Babi na Tara: Shin mai azumi na iya cewa: “Ina Azumi” idan aka zage shi?
377. An karbo daga Ibrahim dan Musa ya ce: “Hisham dan Yusuf ya ba mu labari daga dan Juraij ya ce: Adda’u ya ba ni labari daga Abu Salih Zayyat cewa, lallai shi ya ji Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Allah Ya ce, “Dukkan aikin dan Adam nasa ne face Azumi (domin shi) Nawa ne. Kuma lallai Ni ne Mai sakawa kansa.” Kuma Azumi garkuwa ne. Idan yinin azumin dayanku ya kasance kada ya tara da matarsa kuma kada ya yi fada. Idan wani ya zage shi ko ya fadace shi, ya ce: “Lallai ni, mai azumi ne.” Ina rantsuwa da Wanda ran Muhammad yake hannunSa, warin bakin mai Azumi ya fi kanshi a wurin Allah daga turaren Miski. Kuma lallai mai azumi yana da farin ciki biyu da zai yi: Lokacin da yake buda-baki da lokacin da zai hadu da Ubangijinsa.”

Babi na Goma: Yin azumi ga wanda yake jin tsoron aukawa ga zina
378. An karbo daga Abdan ya ce: Daga Abu Hamza daga A’amashi daga Ibrahim daga Alkamata ya ce: “Wata rana ina tafiya tare da Abdullahi (Allah Ya yarda da shi), sai ya ce: “Mun kasance tare da Annabi (SAW) sai ya ce, “Wanda yake iya aure, to, lallai ya yi aure, domin lallai shi yake kariya ga ido, kuma ya fi tsarewa ga farji. Wanda bai iyawa, to, na hore shi da yin azumi, domin lallai shi ne dandakarsa.”