✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu abin da fina-finan sauran kasashe za su nuna wa fim din Hausa – danjuma FKD

danjuma Salisu wanda aka fi sani da danjuma FKD ya shahara wurin ba da haske a fina-finan Hausa. Ya bayyana wahalar da ya sha kafin…

Danjuma Salisudanjuma Salisu wanda aka fi sani da danjuma FKD ya shahara wurin ba da haske a fina-finan Hausa. Ya bayyana wahalar da ya sha kafin ya samu kansa a halin da yake ciki a yau. A hirarsa da Aminiya ya ce babu wani abu da fina-finan sauran kasashe za su nuna wa fim din Hausa. A sha karatu lafiya:

Za mu fara da tarihinka a takaice.
Assalamu alaikum, da farko sunana danjuma Salisu, amma an fi sanina da danjuma FKD. An haife ni 1 ga watan Oktoba, 1984. Na yi firamare a Magwan Model Primary School. Na yi makarantar sakandare ta Army Day, sannan na yi difloma Kano State Polytechnic, a yanzu haka kuma ina kokarin fara karatun HND.  Maganar iyali kuma har yanzu ina kasuwa.
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin harkar fim?
Alal hakika na dade ina son shiga harkar fim, saboda tun lokacin da na fara ganin maigidana Ali Nuhu a fim sai na ji ya burge ni, na kuma ji sha’awar na shiga harkar a dama da ni. Na shigo harkar ana kyara ta, amma sannu a hankali har na samu karbuwa, a yanzu kuma ake ji da mu a harkar, saboda haka ne ya sa a ko’ina za a ji ina cewa maharkurci mawadaci, wato idan har za ka yi hakuri to komai na rayuwar duniya zai zo maka da sauki. Don haka duk abubuwan da suka faru da ni na manta da su, sun wuce kamar ma ba a yi ba.
Kana nufin akwai abubuwa marasa dadin ji da suka faru da kai a harkar fim kafin ka kai wannan matakin?
kwarai akwaisu amma dai komai ya wuce, kuma ba na so na tono su. Ina fada ne dai kawai don duk wanda ya samu kansa a cikin mawuyacin hali, to ya yi hakuri komai zai wuce.
Ke nan akwai kalubalen da ka fuskanta a harkar?
Komai mutum zai yi a rayuwa ai sai ya fuskanci wasu matsaloli da za su addabe shi. Za ka fuskanci matsaloli, nan daban, can ma daban. Kafin ka samu biyan bukata sai ka sha wahala. Ko manyan da a yanzu ake sha’awarsu a harkar fim din Hausa, idan suka fara ba ka labarin wahalhalun da suka sha kafin sun cim ma burinsu a harkar za ka sha mamaki. Don haka ina yi wa Allah godiya.
Idan aka ambaci sunanka hankalin masu kallo zai tafi bangaren fitila, wato ba da haske yayin daukar fim, shin ko ka shigo harkar fim da wannan kuduri ne ko kuma da ba ka samu abin da kake so ba ne sai ka juya akalarka zuwa fitila?
A gaskiya na shigo harkar fim ne don na zama jarumi, bayan na buga, na buga ne sai na ga babu kanta, hakan kuma ya sa na koma mai rawa a bayan jarumi (background dancer), inda na rika raye-raye a cikin fina-finai, sannu a hankali har na zama yaron Ali Nuhu, inda muka rika fita aiki tare, hakan ne ya sa aka fara ba ni aikin ba da haske. Daga farko zuciyata ba ta gamsu ba, amma a yanzu ina jin dadi, kuma ina ci gaba da ba da haske.
A yanzu za ka iya cewa burinka ya cika ko har yanzu da saura?
Alhamdu lillahi, amma dai da saura. Burina a ce ina daya daga cikin wadanda Kannywood za ta yi bugun kirji da su, ya kasance irin gudunmuwar da za mu ba harkar fim ta zama abar alfahari. Burina in reni wadansu da za su bunkasa Kannywood.
Shin za ka ci gaba da ba da haske ne, ko kuma za ka fara shirya fina-finai, ko kuma za ka juye zuwa babban jarumi?
A gaskiya dukkan abubuwan da ka lissafa babu wanda ba na so na shahara a kai. Amma dai komai a hankali ake binsa, ba kuma a lokaci guda zan yi su ba. Zan bi su ne daga wannan matakin zuwan wannan. Ina da yakinin akwai lokacin da zai zo da zan ajiye ba da hasken domin na reni wadanda za su rika yi.
Lokaci zuwa lokaci kakan fito a cikin fina-finai, zuwa yanzu ka yi fina-finai kamar nawa?
A gaskiya ban san adadin yawan fina-finan da na yi ba. A cikinsu akwai Adamsy, inda na fito direban Adam A Zango. Akwai ‘Ahlil Kitabi’ da ‘dan Marayan Zaki’ da ‘karangiya’ da ‘Habib’ da ‘Jamilun Jiddan’ da ‘Ga Fili Ga Mai Doki’ da ‘Da’u da sauransu.
Wadane nasarori ka cim ma a harkar fim?
Na samu nasarori masu yawa. Ina addu’ar Allah Ya kara ba mu nasara. Allah Ya yi mana maganin wadanda suke so su bata mana harkar. Da kudin fim na sayi fili, na fara gini, na yi karatuna, na sayi abin hawa. Da kudin fim nake taimaka wa iyaye da ‘yan uwa da kuma abokan arziki. Na shirya fim nawa na kaina, sunansa ‘Ta Cuce Ni’. A yanzu kuma ina kokarin shirya wani. Baya ga haka harkar fim ta samu babbar nasarar samun kayan aiki na zamani da suka hada da kyamara da fitilu da ma’aikata da sauransu, kuma babu wani abu da fina-finan sauran kasashen duniya za su nuna wa fim din Hausa, mun fi wadansu fina-finan samun ingantattun labarai.