Da Dumi Dumi

Babu adalci cikin hukuncin Jihar Zamfara – Adam Oshiomhole

Shugaban jami’yar APC na kasa Adam Oshiomhole ya ce babu adalci a hukuncin da kotun koli ta yanke na ba da dukkan kujerun Sanata 3 da 7 na ‘yan Majalisar Wakilai da kujeru 24 na Majalisar Dokoki da kuma kujerar gwamna duk ga  jami’yyar PDP.

Ya bayyana haka ne, lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai, ya ce babu maganar adalci a wannan lamari, bayan  wanda ya samu nasara ba shi aka ba ba, sai aka ba wanda ba shi al’umma suka zaba ba, ya kara da cewa al’ummar Jihar Zamfara sun zabi abin da suke so, amma sai kotu ta ce duk kuri’ar da suka kada ta zama ba ta da amfani, bayan babbar kotu ta tabbatar da cewar ‘yan takararmu an tsayar da su bisa dacewa.

Ya ce idan har adalci a ke so, to kamata ya yi a ce an  ba da damar sake yin zaben, babu wani abu na dimokuradiyya idan aka kakaba wa mutane, ba abin da suka zaba ba ya jagorance su, sai dai abin da muka fahimta shi ne daga kotun koli babu sauran wani batu, don haka dole ne mu bi hukuncin kotun kolin, to amma babu maganar adalci a wannan hukunci ga al’ummar jihar Zamfara a cewarsa.

Share