✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu dalilin da za a ci zarafin magoya bayan APC a Jihar Sakkwato – Maidawa Kajiji

Dan majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Shagari a Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato kuma Shugaban Kwamitin Shari’a na Majalisar Alhaji Maidawa Kajiji ya ce, aikin dan…

Dan majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Shagari a Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato kuma Shugaban Kwamitin Shari’a na Majalisar Alhaji Maidawa Kajiji ya ce, aikin dan majalisa shi ne ya yi doka da kuma sanya ido ga abin da Majalisar Zartarwa ke gudanarwa tare da gudanar da aikin kwamitocin majalisa da kuma gabatar da korafe-korafen jama’ar da yake wakilta ga gwamnati.

Alhaji Maidawa Kajiji ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Sakkwato, inda ya ce, “Bayan da muka shigo Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato ta  9, mun yi dokar kasafin kudi ta 2020, kuma dokar da ta samar da Hukumar Gudanar da Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato mun yi mata gyaran fuska da sauransu.”

Da yake tsokaci dangane da zargin da ake yi wa  ’yan majalisar na Jam’iyyar APC cewa sun zama ’yan amshin Shatan gwamnati ba su yin tirjiya ga bukatun gwamnati, Alhaji Maidawa Kajiji cewa ya yi, “Ba haka ba ne, na yi shekara 16 ina aiki a majalisa kafin a zabe ni dan majalisa, mutane suna kallon yadda muke da Shugaban Majalisa da Shugaban Masu Rinjaye duk da ga shi mu ne ’yan adawa. Don haka bai yiyuwa duk abin da gwamnati ta kawo mu watsa masa kasa, in muka dubi manufofin jam’iyyarmu da wadanda suka zabe mu, za mu kawo koke-kokensu don kawo ci gaba a yankunanmu, in ka yi la’akari da wadannan mun zo ne mu yi abin da zai amfane mu da al’ummarmu don haka ba laifi in mutum ya ga wani abu da ake yi da ba daidai ba ko kuma bai da alfanu ga jama’a ya ki amincewa da shi.”

Ya ci gaba da cewa “Amma mutane su fahimci abubuwan da muke bai wa gwamnati goyon baya abubuwa ne da muke ganin suna taimaka wa jama’a duk da akwai matsaloli wadanda ba a rasa ba musamman ga magoya bayanmu na APC, ana yi masu sauye-sauyen wajen aiki don cin zarafi, ba don doka ta aminta a yi ba.  Ka ga an dauke ma’aikaci domin ya goyi bayan jam’iyyarmu an kai shi inda ba a bukatarsa ko bukatar aikinsa, can kuma inda aka dauke shi ba a kawo wani madadinsa ba kuma ana bukatar aikinsa. Misali a Karamar Hukumar Gwadabawa asibitinsu an dauke ma’aikata 26 an raba su zuwa wasu kananan hukumomi ba a kawo wadansu ba. ’Yan majalisarsu sun yi ta koke-koke kan wannan amma ba wani mataki da aka dauka. A Karamar Hukumar Shagari akwai wadanda aka rike wa albashi, akwai hakimai 9 da uban kasa daya sai daga baya aka ci gaba da biyansu.”

Ya ce, akwai wani malami da aka dauke daga Sanyin-Lawal aka kai shi Horo kuma aka daina biyansa albashi, ya ce “Muhimmancin karantarwar da yake yi ta sanya na rika biyansa albashi a cikin aljihuna duk da cewa ya kai mataki na 7 tunda aka yi zaben Shugaban Kasa ba a sake ba shi albashi ba, ba ruwansu da wahalar da yake ciki.”

Haka kuma ya bayyana matsayin ’yan majalisar APC a majalisar game da bashin Naira  biliyan 65.7 da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal zai ciwo inda ya ce wannan bashin da ake magana a kafafen watsa labarai jita-jita ne domin har yanzu maganar ba ta zo gaban majalisa ba, saboda suna hutu kuma ba a kira su aka ce musu ga maganar ba.