Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Babu hadarin daukar coronavirus sosai a jirgi

Babu hadarin daukar coronavirus sosai a jirgi

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika ya ce matukar matafiya sun sa takunkumi a jirgin sama to hadarin su kamu da cutar coronavirus don sun zauna kusa da juna kadan ce.

Ya bayyana haka ne bayan jama’a sun nuna damuwa kan rashin bayar da tazara a kujerun jiragen sama bayan bude filin jirgi na Malama Aminu Kano a ranar Asabar.

“Zama a cikin jirgin zama na da cikakken kariyar lafiya. Muddin ka sa takunkumi, to ba ka cikin hadari a duk inda ka zauna”, a cewar Ministan.

Ya ce an gina jirgin sama ne ta yadda duk bayan minti biyu ake kashe kwayoyin cuta a cikinsa ta hanyar zafin da iskar cikinsa ke yi da ya kai digiri 100, wanda babu kwayar cutar da ke iya rayuwa a ciki.

Hadi Sirika kya bayyana gamsuwa da matakan kariyar COVID-19 da ya gani an dauka a filin jirgin Malam Aminu Kano.

Ya kuma sanar da cewa dukkan filayen jiragen sama 22 a fadin Najeriya za su ci gaba da jigilar fasinja na cikin gida daga ranar 15 ga watan Yuli, domin a cewarsa sun cika ka’idojin da ka gindaya na kariyar cutar coronavirus.

A ranar 8 ga wata ne aka sake bude filayen jiragen sama na Legas da Abuja, bayan an rufe bangaren sufurin tun ranar 27 ga watan Fabrairu a fadin Najeriya sakamakon bullar cutar coronavirus.

A ranar Asabar 11 ga watan Yuli kuma aka bude filayen jirgi na Kano da Ibadan, da Fatakwa da Benin da Kuma Maiduguri.