Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Babu imani ga mai cutar da makwabcinsa (1)

Babu imani ga mai cutar da makwabcinsa (1)

Daga Hudubar  Malam Bashir Salihu Abuga

Limamin Masallacin Izala, Kalaba

Fassarar Salihu Makera

 

Huduba ta Farko:

Hamdala da taslimi.

Baya haka ya ku mutane! Ku bi Allah da takawa a kan hakkin binSa, kada ku yarda ku mutu face kuna masu sallamawa (Musulmi).

Ya ku bayin Allah! Ayoyi da hadisai sun karfafa hakkin makwabci a kan makwabcinsa. Jibrilu (AS) bai gushe ba yana yi wa Annabi Muhammad (SAW) wasiyya a kan makwabci har sai da Annabi (SAW) ya yi tsammanin makwabci zai yi tarayya da makwabicnsa a cikin gado. Don haka babu mai munana wa makwabci ya cutar da shi face la’imi marar son alheri kuma abin kyama. Mai aikata dukkan fasadi a bayan kasa. Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Wallahi bai yi imani ba! Wallahi bai yi imani ba! Wallahi bai yi imani ba! Aka ce, “Ya Manzon Allah! Hakika wannan kuwa ya tabe kuma ya yi asara, wane ne shi?” Ya ce: “Wanda makwabcinsa bai kubuta daga bawa’ikahu ba. Suka ce: “Mene ne bawa’ikahu?” Ya ce: “Sharrinsa.”

Larabawa sun kasance a zamanin Jahiliyya da kuma bayan zuwan Musulunci suna kiyaye amana, suna alfahari da kyautata makwabtaka. Kuma gwargwadon kirkin makwabci gwargwadon tsadar gidan da yake makwabtaka da shi. Musulunci yana umarni da kyautata makwabtaka koda ga kafirai ne. Mafi sharrin mutane shi ne wanda mutane suke gudunsa saboda tsoron sharrinsa. Suke nesa da shi saboda sanin sharrinsa don gudun cutarwarsa. Mafi munin makwabci, shi ne wanda ke bibiyar sirri da gazawar makwabcinsa, yake bin al’aurori don fitar da sharri da baza shi. Wannan ba abin amincewa ba ne a addini da rayuwa da iyali da dukiya. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya kasance ya yi imani da Allah da Ranar Lahira, to, ya girmama makwabcinsa, kuma wanda ya kasance ya yi imani da Allah da Ranar Lahira, to, ya girmama bakonsa, kuma wanda ya kasance ya yi imani da Allah da Ranar Lahira, to ya fadi alheri ko ya yi shiru.” Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mumini, shi ne wanda mutane suka aminta da shi. Musulmi kuma shi ne wanda Musulmi suka kubuta daga harshensa da hannunsa, mai hijira kuma shi ne wanda ya kaurace wa mugun abu. Na rantse da Wanda raina yake hannunSa, wanda makwabcinsa bai kubuta daga sharrinsa ba, ba zai shiga Aljanna ba!”

Abin kunya ne gare ka ya kai Musulmi! A ce ka kwana a koshe, amma makwabcinka ya kwana da yunwa! Abin kunya ne gare ka a ce ka yi sababbin tufafi amma ka yi rowar tsofaffin tufafinka ga makwabtanka marasa tufafi! Kuma abin kunya ne gare ka a ce kana jin dadi da daddadan abinci da abin sha, amma makwabtanka suna neman kasusuwa da ragowar abinci, alhali kana sane da fadin Manzon Allah (SAW): “Kada makwabciya ta raina abin da za ta ba makwabciyarta koda kashin hakarkarin akuya ne kuwa.” Kuma ya ce da Abu Zarri (RA): “Ya Abu Zarri idan kana dafa nama ka yawaita ruwan (romo) don ka ba makwabtanka.”

Ya kai Musulmi! Lallai daga cikin hakkokin makwabci a kanka akwai cewa, ka yi masa sallama idan ka hadu da shi, kuma ka je gaida shi idan ba ya da lafiya, kuma ka raka gawarsa idan ya rasu, kuma ka kasance uba ga ’yan’yansa bayan rasuwarsa kamar yadda shi ya kasance musu a rayuwarsa. Ka tsaya a gefensa (tare da shi) a cikin kunci da yalwa da tsanani da wadata. Wata maganar hikima na cewa: “Wanda amfanar da ’yan uwansa ta kubuce masa, kada ya yarda amfanar da makwabcinsa ta kubuce masa!”

Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mafi alherin aboki a wurin Allah Madaukaki, shi ne wanda ya fi alheri ga abokinsa, kuma mafi alherin makwabci a wurin Allah Madaukaki shi ne wanda ya fi yin alheri ga makwabcinsa.”

Haram ne a kanka ya kai Musulmi! Ka rika leka gidan makwabcinka alhali bai sani ba, ko ka ha’ince shi game da iyalinsa. Duk wanda ya leka gidan makwabcinsa ba tare da izininsa ba, Allah zai cika idonsa da wutar Jahannama. Kuma haram ne a gare ka rika kashe kunne domin ka  ji abin da yake fada a cikin gidansa ka zama kamar mai leken asiri da maganarsa da aikinsa ba za su kubuta daga gare ka ba.

Kuma idan ba za ka iya kyautata wa makwabcinka da dadada masa ba, to ka kame daga cutar da shi, kada ka cutar da shi koda da gaisuwa don ya samu ya huta a cikin gidansa. Idan ya kira ka, ka amsa masa, idan ya nemi shawararka ka ba shi shawara tagari, idan aka zalunce shi ka taimaka masa, idan shi yake zaluncin, ka hana shi. Idan ya kyautata ka gode masa, idan ya munana ka yi masa afuwa, idan ya aikata fasadi kada ka karfafa shi a kai, domin da yawa makwabci zai rike wuyan makwabcinsa a Ranar Kiyama ya ce: “Ya Ubangijina! Lallai ne wannan ya rufe min kofarsa, ya ki yi min nasiha, ya gan ni ina aikata sharri bai hana ni ba.” Wani mutum ya ce, “Ya Manzon Allah! Lallai ana ambaton yawan Sallar wance da azuminta, sai dai tana cutar da makwabcinta.” Sai ya ce: “Tana cikin wuta!” Sai ya ce: “Ya Manzon Allah! Lallai wance ana cewa tana da karancin Sallah da azumi, amma tana yawan sadaka… kuma ba ta cutar da makwabtanta.” Sai (SAW) ya ce: “Tana cikin Aljanna.”

Manzon Allah (SAW) ya ce: “Abubuwa hudu suna daga cikin sa’ada: mace tagari da gida yalwatacce da makwabci nagari da abin hawa mai lafiya. Kuma abubuwa hudu suna cikin shakawa(tabewa da rashin sa’a): mugun makwabci da muguwar mace da mugun abin hawa da kuntataccen gida.”

Allah Madaukaki Yana son makwabcin da ya yi hakuri da cutarwar makwabcinsa har Allah Ya isar masa ta sauya masa ko mutuwa. Mutuwa hanya ce da ba makawa.

Ya bayin Allah!  “Lallai ne Allah Yana umarni da adalci da kyautatawa da ba ma’abucin zumunta (hakkinsa), kuma Yana hani daga alfasha da abin ki da zalunci, Yana yi muku wa’azi tsammaninku za ku yi tunani.” Don haka ku tuna Allah Mai girma da Daukaka, sai Ya tuna da ku, kuma ku gode maSa a bisa ni’imominSa, sai Ya kara muku. Kuma ambaton Allah ne Mafi girma. Kuma Allah Yana sanin abin da kuke aikatawa.