Search
Subscribe
Babu kyau Musulmi ya ci bashi don yin layya – Ustaz Auwal Abdulkarim

Malam Auwal Abdulkarim Limamin Masallacin Mopol 11 Kalaba

Babu kyau Musulmi ya ci bashi don yin layya – Ustaz Auwal Abdulkarim

Wannan wata na Zul-Hajji wata ne da Musulmin da Allah Ya huwace masa yake sayen abin yanka domin ya yi layya. Layya Sunnah ce da ta samo asali daga Annabi Ibrahim (AS). Wannan ya sa Musulmi kan sayi abin da za su yi layya domin koyi da Manzon Allah (SAW). Sai dai yayin da wadansu ke yin layya domin kwadayin lada wadansu kuma suna neman mayar da abin gasa ko al’ada su ce sai sun ci bashi domin su yi layyar kada ta wuce su. Wakilin Aminiya a Kalaba ya tattauna da Limamin Masallacin Barikin ’Yan sandan Kwantar da Tarzoma (Mopol) da ke Kalaba Ustaz Auwal Abdulkarim, inda ya ce kuskure ne Musulmi ya ci bashi domin ya yi layya:

 

Malam wadanne abubuwa ne sharuddan layya?

Bismillahir Rahmanir Rahim Allahumma Salli ala nabiyina Muhammad wasallim. Bayan haka lallai layya tana da sharudda da shari’a ta gindaya musamman a kan dabbar da za a yi layyar da ita. Abin da ya shafi tumaki da awaki, Sunnah ta Ma’aiki (SAW) ta tabbatar da cewa, idan rago ne akalla ya cika wata 6 zuwa sama, idan kuma akuya ce ko bunsuru ya zamo ya cika shekara guda.

Abin da ya shafi shanu da rakuma su ma akwai adadi da shari’a ta tabbatar sai sun kai wadannan shekaru  a yi layya da su. Kuma layya da rago ya fi falala da soyuwa a kan layya da tunkiya, layya da tunkiya ya fi falala a kan layya da bunsuru ko akuya, layya da bunsuru da akuya ya fi falala a kan yin layya da saniya ko rakumi. Layya na amfani ne da karamar dabba. Ita kuma babbar dabba an fi so a gabatar da ita wajen hadaya. Har ila yau yana daga cikin Sunnah ta Manzo (SAW)  idan ka tabbatar za ka yi layya to ana so tun kafin Zul-Hajji ya kama idan akwai abin da za ka yi na gyaran fuska ko farce to ka yi tun a cikin watan Zul-Kida, da zarar Zul-Hajji ya shiga ana so ka kame daga yin aski da gyaran fuska da yanke farce har sai ka gabatar da layyarka .

Wadanne ne kwanakin layya?

Layya ana yin ta ce a Ranakun Haske wato ranakun 10 da 11 da 12 da 13 na Zul Hajji. A wadannan ranaku ne ake yin layya duk wanda bai samu ya gabatar a wadannan ranaku ba to sai ya yi hakuri har Allah Ya kai mu badi.

Ya halatta Musulmi ya ci bashi domin ya yi layya?

A’a bai halatta ba, don Annabi (SAW) ya ce addini sauki ne. Bai halatta ba tunda ba wajiba ba ce tana cikin Sunnar Manzon Allah  (SAW) ga wanda Allah Ya hore masa. Saboda haka ba wajibi ba ne idan ba ka da abin layya ka ce sai ka je ka rikito bashi don ka gabatar da layya, wannan bai halatta ba, ba gwaninta ba ne a addinin Musulunci.

Mene ne hukuncin mutumin da ya dauki wata kadara tasa ya bayar jingina ko ya ci bashi domin ya sayi abin layya?

To layyar ta yi amma duk da haka ya yi abin da ba a  so ba. Manzo (SAW) ya ce mana ‘addini sauki ne’ idan ba ka da shi babu wani wuri da aka ce ka je ka ciwo bashi sai dai idan ka tabbatar cewa, kana da wasu kudadenka kuma kana da wasu harkokinka kana da yakinin koda ka dauki bashi za ka iya biya. Amma idan ba ka da kudi ko hanyarsu ka ce za ka dauki bashi domin ka yi layya ko ka dauki wani abu naka ka bayar jingina domin ka yi layya wannan ba daidai ba ne ba ka burge Musulunci ba.

 

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin