✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu ranar bude iyakokin Najeriya – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce har yanzu bai sa ranar bude iyakokin Najeriya da aka rufe ba, har sai an shawo kan matsalar shigo…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce har yanzu bai sa ranar bude iyakokin Najeriya da aka rufe ba, har sai an shawo kan matsalar shigo da kayan da aka haramta a kasar.

Shugaban Buhari ya bayyana haka ne lokacin da ya gana da wata tawagar dattijan Jihar Katsina a mahaifarsa ta Daura, kamar yadda mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya bayyana a shafinsa na Twitter.

Ya kuma ce yawan man fetur da ake amfani da shi a kasar ya ragu da kusan kashi 30 cikin 100 bayan da aka rufe iyakokin kasar.

Malam Garba Shehu ya ce Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari za ta yi amfani da irin matakan da ta dauka wajen rufe iyakoki don farfado da bangaren noma.

Ya ce hakan zai sa kasar ta adana biliyoyin Nairori da a baya take kashewa wajen biyan harajin shigo da kaya.

Garba Shehu ya ce Shugaba Buhari ya jinjina wa Shugaba Muhammadou Youssoufou na Jamhuriyar Nijar kan korar wasu jami’ai da kuma haramta ajiye kayan da ake shirin yin fasa kwabrinsu zuwa Najeriya.

Garba Shehu ya ce Shugaba Buhari ya tausaya wa mazauna garuruwan da ke kan iyakoki bisa haramta sayar da man fetur a garuruwansu kuma ya ce gwamnatinsa ta dauki wannan matakin ne don “kare martabar manoma”.

Ya ruwaito shugaban da cewa “rashin gaskiya ya zama ruwan dare a kasarmu.”

Haramcin sayar da man fetur a wadannan garuruwa dai ya janyo rufe duka gidajen mai a yankunan kuma wannan haramcin ya shafi har da Daura, mahaifar Shugaba Buhari.

Buhari ya ce haramtawar na dan wani lokaci ne kafin Hukumar Kwastam ta tantance ainihin masu sayar da mai da kuma gidajen man da ake amfani da su wajen fasa kwabrin haramtattun kaya.