Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Babu siyasa a batun hako mai a Bauchi – Baru

Dokta Maikanti Kachalla Baru
Dokta Maikanti Kachalla Baru

Babban Manajan Daraktan Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) Injiniya Maikanti Kachalla Baru ya ce aikin hako mai a yankin Bauchi da Gombe da gaske suke yi babu batun siysa a ciki, inda ya ce yanzu haka suna hadin gwiwa da wani kamfanin kasar China ne, inda ya ce za su yi tono mai zurfin kafa 14,500 don tabbatar da an samo man a cikin kwana 60 zuwa 70. Dokta Maikanti Baru ya amsa tambayoyin wakilinmu kan wannan aiki da ake yi don ganin an fara hako albarkatun mai a yankin:

Me za ka ce kan aikin fadada binciken man fetur a yankin jihohin Bauchi da Gombe?

ADVERTISEMENT

Wannan rijiyar mai ta Kolmani ta Biyu daya ce daga cikin rijiyoyin mai da gas guda hudu da Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya yi niyyar fara hakar mai a cikinta a bana. Haka kuma za a ci gaba da bincike a rijiyar mai ta Kolmani ta Daya da rijiyar mai ta Nasara ta Daya da kuma rijiyar Kuzari ta Daya.

A 1999 Kamfanin Mai na Shell ya fara tono don gano albarkatun mai a yankin, an ce an samu albarkatun gas da yawa amma bai kai yadda za a yi kasuwanci da su ba. Amma lokacin da aka karanta sakamakon binciken da suka yi sai aka ga ba su zurfafa binciken da suka yi ba ne domin ba su tafi can kasa ba a tonon da suka yi. Saboda haka ne yanzu muka zo don fadada binciken da muke yi, yanzu muna duba nisan kilomita cikin karkashin kasa wanda ba wanda ya isa wannan wurin a binciken da aka yi a baya. Saboda haka tono mai zurfi ne kawai zai iya tabbatar da ko akwai albarkatun mai a wurin kuma shi ne zai tabbatar mana da hukuncin da muka yanke bisa kwarewa na cewa za a iya samun mai da za a hako a yankin.

ADVERTISEMENT

Akwai wurare shida da muka kebe muke kyautata zaton za a samu mai akwai rijiyar Kolmani ta Uku wadda ita ce za mu koma aikin tono don nemo mai a cikinta tsawonta bai wuce kilomita 1.7 zuwa kilomita biyu ba.  Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa an aiwatar da umarnin da Shugaban Kasa ya bayar na kara samo wuraren da za a rika hako mai da kuma Iskar Gas ba.

Wane tabbaci za ka bayar na samun mai a wannan yanki?

Kamfanin NNPC, kamfani ne na zamani ingantacce kuma muna amfani da kayyakin aiki na zamani da fasaha mai inganci. Mun fara wannan binciken man fetur ne tun daga tushe inda muka fara binciken yadda ya kamata. Kuma mun dauki samfuri daban-daban na abubuwan da suka kamata a bincika ko akwai alamar man fetur, mun kuma gudanar da bincike kan yanayin muhallin da ingancinsa da gurbacewarsa,  mun yi bincike kan albarkatun mai har guda uku daban-daban da z asu nuna alama kuma su tabbatar da alamomin wuraren da akesamun mai kuma dukan binciken da muka yi ya nuna cewa akwai albarkatun mai a wurin. Mun kuma kawo wata na’ura ta zamani wadda mafi yawan kayayyakinta suna sarrafa kansu ne (automatic) kuma da wannan na’ura daga dakin da ake kula da dukan ayyuka za mu iya kula da dukan ayyukan da ake gudanarwa na binciken rijiyoyin man. Wannan yana nuna muku irin kayayyakin aiki na zamani da muke da su. Saboda haka muna amfanin da sababbin kayayyakin tono na zamani don mu tono ramin binciken kuma wannan injin tono na zamani zai iya tafiya nisan kafa dubu 20 a cikin kasa. Wanda inda tsohon injin tonon ne da wuya zai iya kaiwa kafa dubu goma, amma da wannan sabon injin tono na zamani za mu iya tono zuwa kafa dubu 20.

Wadanne alamu kuka gani na samun mai?

Gaskiya saboda irin sababbin kayayyakin da muke da su na bincike da hakar mai irin na zamani masu inganci kuma masu sarrafa kansu, mu kanmu mun tabbatar da irin alamun da muka gani a wurin, kuma mun ga alamun nasara wanda kuma da ikon Allah za mu samu nasara kan wannan aiki.

Babbar matsalar da ake samu da tonon mai ita ce lalata muhalli ko kun yi la’akari da haka?

Kwarai da gaske kuwa mun yi la’akari da haka, shi ya sa na ce kamfanoninmu na zamani ne kuma suna da kayayyakin aiki na zamani, mafi yawansu masu sarrafa kansu ne, kuma kamfanonin da ake yayinsu a duniya. Mun gudanar da aikin bincike na tsawon shekara biyu, wannan bincike da muka yi mun binciki yanayin muhallin wuraren da ake zaton samun man, mun ga yanayin muhallin da yanayin kasar, mun kuma gwada shi da irin ayyukan da za mu yi a yankin da kuma yadda zai shafi muhalli da nufin cewa idan muka kammala aikni za mu sake gyara muhalli mu dawo da shi kamar yadda yake a baya. A gaskiya za mu yi iyakacin kokarinmu mu ga cewa bai lalata muhallin ba.