✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu tallafin da mawakan APC  suka samu daga gwamnati  – Murtala Mamsa

Murtala Abdullahi Mamsa Jos shi ne Mataimakin Shugaban Kungiyar Mawakan Jam’iyyar APC da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta Kasa. A tattaunawar da ya yi wakilinmu…

Murtala Abdullahi Mamsa Jos shi ne Mataimakin Shugaban Kungiyar Mawakan Jam’iyyar APC da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta Kasa. A tattaunawar da ya yi wakilinmu ya bayyana cewa Jam’iyyar APC ba ta cika alkawuran da ta dauka musu ba:

 

A matsayinku na Mawakan Shugaban Muhammadu Buhari da Jam’iyyar APC wane tallafi kuke samu a wannan gwamnati?

Babu wani tallafi da muka samu a wannan gwamnati, tun  daga lokacin da ta hau kan mulki zuwa yanzu. Yawancinmu muna nan sama da mutum 20, yanzu  wani a cikinmu ma ba ya da abincin da zai ci. Akwai wadanda suke da motocin kansu a wancan lokaci, amma yanzu abin da za su ci ya gagare su.

Ba kudi ake ba mu mu yi wakoki ba a lokacin, mun yi wakokin ne domin mu bayar da gudunmawarmu ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Duk mutanen da suke taimaka mana a lokacin da muke yi wa Shugaba Muhammadu Buhari wakoki, babu wanda aka bai wa wani mukami da za mu je mu kai masa kuka.

Ganin yadda wannan gwamnati take tafiyar da mulkin kasar nan, kana ganin jam’iyyarku ta APC za ta samu nasara a zaben gaba?

Ni abin da na lura da shi a zuwan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da gwamnati APC kamar an rusa dimokuradiya ce a kasar nan. Sai dai ba mu san me za su yi daga gobe zuwa jibi ba. Amma a shekara biyar da gwamnati ta yi  babu wani aiki daya da ta fara ta kammala.  Ina tabbatar maka wadanda suka bi tafiyar Shugaba Muhammadu Buhari dodar, babu wanda zai sake yi wa wani wahala a siyasa kamar yadda aka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari.

Domin Akwai wadanda suka rasu ko jaje ba a yi wa iyalansu ba, akwai wadanda suka narkar da kudinsu wajen kafa wannan gwamnati amma su ma ba a taimake su ba. Sakamakon wadannan abubuwa da suka faru, yanzu ina tabbatar maka cewa duk wata siyasa ta kishi an bar ta a Najeriya.

Yanzu a Najeriya babu talakan da zai kara yarda ya je ya wuni ko ya kwana, kan layin zaben wani dan takara. Domin Jam’iyyar APC ta karya wa duk wani talakan Najeriya alkawari da ta yi masa.

A wa’adin farko talakawan Najeriya sun yi sak lokacin zabe suka zabi wadanda ba su yi wa al’ummar Najeriya komai ba. Yanzu ma ga shi an kara yin sak! To ina tabbatar maka wadanda aka zaba a zaben wa’adin farko a tsarin sak, sun fi wadanda aka zaba a tsarin sak na wannan karo. Domin kashi 90 na wadanda aka zaba a karkashin Jam’iyyar APC sun kashe makudan kudi ne, kafin su samu damar tsayawa takara, suka kayar da ’yan takara masu kyau. Don haka matsalar da za a fuskanta da wadannan ’yan majalisa sai ta fi matsalar da aka fuskanta da ’yan majalisar baya.

Ya kamata gwamnati ta tashi tsaye ta rage wa al’ummar Najeriya radadin da suke ciki, domin al’ummar Najeriya suna cikin wani yanayi na wahala. Babu shakka idan gwamnati ba ta fito ta taimaki jama’a ba, an ci amanarsu.

Wadanne hanyoyi kake ganin gwamnati za ta bi ta gyara wadannan matsaloli?

Abin da ya kamata shi ne ta koma ta nemo wadanda suka yi mata wahala, ta kyutata musu. Kuma kamar yadda na fada a baya, gwamnatin nan ta rage wa al’ummar Najeriya radadin da suke ciki, domin al’ummar Najeriya suna cikin wahala.

Wane sako kake da shi zuwa ga al’ummar Najeriya?

Sakona ga  al’ummar Najeriya shi ne su fahimci wannan al’amari da ya faru, ya zamanto darasi gare su. Nan gaba idan za mu so abu, kada mu cika zakewa wajen nuna soyayya, kan duk wani abu da ya zo mana.