✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu wadansu ’yan hana ruwa- gudu a fadar Shugaban Kasa – Shugaban MBO – DSG

Shugaban Kungiyar Goyon Bayan Ci gaban Muhammadu Buhari da Osinbajo (MBO-DSG) ta Kasa Alhaji Usman Ibrahim ya ce suna goyon bayan ci gaba da kasancewar…

Shugaban Kungiyar Goyon Bayan Ci gaban Muhammadu Buhari da Osinbajo (MBO-DSG) ta Kasa Alhaji Usman Ibrahim ya ce suna goyon bayan ci gaba da kasancewar Abba Kyari a matsayin Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Kasa da kuma sauran masu rike da mukamai a wannan gwaamnati.

Usman Ibrahim ya bayyana haka ne a taron zanga-zangar nuna goyon baya da suka gudanar a Sakatariyar Jam’iyyar APC a ranar Talatar da ta gabata, domin mai da martani ga wata zanga-zangar da wadansu matasan Jam’iyyar APC suka gudanar a ranar Litinin da ta gabata, inda suka bukaci Shugaba Buhari ya hanzarta sauke Abba Kyari da rabuwa da Alhajo Mamman Daura daga cikin tafiyar gwamnatinsa, inda suka ce su ne ke hana ruwa-gudu wajen tafiyar da harkokin gwamnati. Kuma sun yi zargin cewa rashin tabuka wani abin kirki da Gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi a zangon farko duk ya rataya ne a wuyansu. Shugaban Kungiyar Ci gaban Buhari da Osinbajo,(MBO-DSG) wanda ya jagoranci masu zanga- zangar ya ce wannan lamari babu kamshin gaskiya a ciki, domin babu wadansu da ke hana ruwa-gudu a fadar Shugaban Kasa.

Da yake jawabi ga manema labarai, Shugaban  ayarin ’ya’yan Jam’iyyar APC da suka gudanar da zanga-zangar, Alhaji Usman Ibrahim, cewa ya yi sanin kowa ne Shugaba Buhari ya mulki kasar nan a zangon farko na mulkinsa a 2015, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaban da kasar nan take bukata, musamman wajen aiwatar da ayyukan raya kasa. Ya kara da cewa sanin kowa ne kowace gwamnati tana zuwa da irin  mutanenta, wadanda suke ba da gudunmawarsu wajen ci gabanta, amma abin mamaki wadansu sun fito suna zargin irin wadannan mutane da ke cikin wannan gwamnati, wanda kowa ya san hazikai ne saboda irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban al’ummar wannan kasa. Ya ce Shugaban Kasa shi ke da ikon ya nada mataimakansa, masu ba shi shawara da kuma ministocin da yake son ya yi aiki da su.

Ya ce zargin da ake yi cewa akwai mutanen da suka dabaibaye Shugaba Buhari, suka hana shi yin komai shiri ne kawai na bata suna “Babu wadanda suka hana al’amuran gwamnati tafiya, kuma sanin kowa ne cewa a tarihin siyasar kasar nan, kowacce irin gwamnati tana zuwa da mutanenta, amma babu wacce aka zarga da  cewa mutanenta sun yi tarnaki sun hana ruwa gudu, sai a wannan gwamnati, hakan ba zai kasance alheri ga ci gaban kasa ba, kuma masu yin wannan zargi, sun kasa gabatar da shi bisa tsarin da ya dace,’ inji shi.

Da yake karbar masu zanga- zangar Babban Mai Binciken Kudi na Jam’iyyar APC, a madadin Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Cif George Moughalu, ya ba su tabbacin zai gabatar da sakonsu ga mambobin Kwamitin Zartarwa na Jam’iyyar APC ta Kasa.