✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bacewar dan jaridar Saudiyya a Turkiyya: Akwai Bahaushe cikin wadanda ake zargi

Yayin da kasar Turkiyya ta fara zargin  Saudiyya da kashe fitaccen dan jaridar nan Jamal Khashoggi wanda ya bace bayan da aka yi masa gani…

Yayin da kasar Turkiyya ta fara zargin  Saudiyya da kashe fitaccen dan jaridar nan Jamal Khashoggi wanda ya bace bayan da aka yi masa gani na karshe a Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke birnin Istanbul na kasar Turkiyya, wasu bayanai sun nuna cewa akwai Bahaushe a cikin mutum 15 da suka shigar Turkiyya don aiwatar da abin da Turkiyya ke zargi.

Jamal Khashoggi ya yi fice wajen caccakar kasar Saudiya da kuma aikace-aikacen Yarima Muhammad bin Salam, mai jiran gado na kasar.

Tuni  kasar Saudiyya ta musanta wannan zargin, inda ta ce za ta hada hannu da kasar Turkiyya wajen bincike a kan lamarin.

Yadda ake zargin lamarin ya auku

Gwamnatin Turkiyya ta yi imanin cewa kashe dan jaridar mai kimanin shekara 59 aka yi a makon jiya a karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin  Istanbul.

Muryar Amurka ta ruwaito budurwar Khashoggi, Hatice Cengiz, tana bayyana cewa ta jira shi a harabar karamin ofishin Jakadancin Saudiyya a ranar Talata, inda ta ce lallai bai fito daga ginin ba tunda ya shiga. ’Yan sandan kasar Turkiyya sun ce wadansu mutanen Saudiyya kimamin 15 sun shigo birnin Istanbul ta jiragen sama biyu a ranar Talatar da ta gabata, kuma sun kasance a karamin ofishin Jakadancin Saudiyyar a daidai lokacin da Khashoggi yake ciki.

Mutanen  su ne Meshal Saad M Albostani da Salah Muhammed A Tubaigy da Naif Hassan S. Alarifi da Muhammed Saad H. Alzahrani da Mansur Othman M. Abahüseyin da Halid Aedh G. Altaibi da Abdulaziz Muhammed M. Alhawsawi (wanda ake kyautata zaton Bahaushe ne) da Waleed Abdullah M. Alsehri da Türki Müşerref M. Alsehri da Thaar Ghaleb T. Alharbi da Maher Abdulaziz M. Mutreb da Fahad Shabib A. Albalawi da Badr Lafi M. Alotaibi da Mustafa Muhammed M. Almadani da Saif Saad K Alkahtani.

Shugaban Turkiyya Racep Tayyip Erdogan ya bayyana wa manema labarai cewa, “Ina bin diddigin al’amarin kuma za mu sanar da duniya sakamakon binciken da aka yi a hukumance.” Sannan ya kara da cewa, “Da yaddar Allah, ba za mu fuskanci al’amarin da ba mu so ba.”

Shugaba Erdogan ya kara da cewa ’yan sanda na nazarin faye-fayen bidiyon tsaro da ke mashigar karamin ofishin jakadancin da kuma na filin jirgin saman Istanbul.

Turkiyya ta nemi izinin Saudiya don bincikar ofishin jakadancinta

A wani bangaren kuma, Shugaban  Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bukaci kasar Saudiyya ta ba kasar Turkiyya izinin ta binciki ofishin jakadancin kasar da ke Istanbul.

Shugaba Erdogan ya bayyana haka ne a lokacin da yake ziyara a Budapest, babban birnin kasar Hungary, inda ya ce, “Lallai ne za mu samu sakamakon wannan bincike cikin gaggawa.”

A nasa bangaren, Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman ya ce a shirye kasar Saudiyya take ta tarbi gwamnatin Turkiya tare da ba ta cikakken goyon baya wajen gudanar da binciken da take bukata a ofishin jakadancinta, saboda a cewarsa, “Babu wani abu da take boyewa, game da bacewar  Jamal Khashoogi.” Duk da cewa jami’an Saudiyya sun bayyana cewa zargin hannun Saudiyya a bacewar dan jaridan kanzon kurege kawai ba dai ba makama.

Dole Saudiyya ta wanke kanta- Shugaban Turkiyya

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kara da cewa tilas kasar Saudiyya ta fito fili ta wanke kanta ta hanyar bayar da shaidar da ke nuna cewa lallai Khashoogi ya bar ginin ofishin jakadancinta bayan ya isa ofishin a ranar Talatar makon jiya domin karbar takardun daurin aurensa da yake shirin yi, domin matar da yake niyyar aure din Hatice Cengiz da take jiransa a wajen ofishin ta tabbatar bai fito daga cikin ginin ba.

Wane ne Jamal Khashoggi?

Kafar Labarai ta BBC ta rairayo takaitaccen tarihi da gwagwarmayar Jamal Khashoggi inda ta ce:

Jamal Khashoggi, mai shekara 59 ya fara aikin jarida ne a Saudiyya bayan da ya samu digirinsa a Amurka a 1985.

Jamal Khashoggi ya fara aikin jarida tun yana da kuruciya a matsayin mai aika rahotanni, lokacin da ya kulla abota da Osama bin Laden a zamowarsa mai adawa da Saudiyya, abin da ya sanya shi barin kasar.

Kafin bacewarsa a ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Istanbul, gudun hijirar da Khashoggi ya yi na nufin yana raba lokacinsa tsakanin Amurka da Birtaniya da Turkiyya.

Ya bar Saudiyya a watan Satumban shekarar 2017, bayan da suka samu tangarda da mahukuntan masarautar Saudiya.

Daga kasashen waje, ya ci gaba da yada ra’ayoyinsa masu sukar gwamnatin Saudiyya, ta makalar da yake rubutawa a jaridar Washington Post ta Amurka da kuma a shafinsa na Twitter inda yake da mabiya miliyan 1 da dubu 600.

Lokacin da yake aiki da jaridar al-Madina a shekarun 1990, ya yi rubutu sosai a kan masu ikirarin jihadi a Afghanistan da suka shiga kasar don yakar Sobiyet.

Ya yi hirarraki da dama musamman da Osama bin Laden, wanda ya ruwaito cewa ya san shi tun yana matashi a Saudiyya.

A lokacin, Bin Laden bai yi kaurin suna a kasashen yamma a matsayin shugaban Al-Ka’ida ba.  Khashoggi ya ziyarce shi a tsaunukan Tora Bora, kuma ya yi hira da shi a Sudan a 1995.

Jaridar Jamus, Der Spiegel ta yi hira da Khashoggi a 2011 kan alakarsa da Osama bin Laden. Khashoggi ya amince cewa ya kasance mai ra’ayi daya da bin Laden a baya, ta amfani da hanyoyin da suka kaucewa dimokuradiyya, kamar shisshige wa tsarin siyasa ko amfani da hanyoyin tashin hankali don kwato wa yankin Larabawa ’yancinsu daga gwamnatocinsu masu cike da cin hanci da rashawa.