✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Badakalar cin hanci da rashawa ta addabi kasar Malawi

Badakalar cin hanci da rashawa ta addabi kasar Malawi, inda a kalla jami’an gwamnati 10 ake tuhuma da laifin cin hanci da rashawa. An kuma…

Badakalar cin hanci da rashawa ta addabi kasar Malawi, inda a kalla jami’an gwamnati 10 ake tuhuma da laifin cin hanci da rashawa. An kuma samu wani daga cikinsu ya boye Dala dubu 25 a gidansa, da wanda ya cusa daurin kundin banki a mazubin kayan motarsa.
Ana tuhumar jami’an gwamnatin kasar da amfani da mukamansu wajen cin hanci da rashawa.
A watan da ya wuce, an daure babban jami’in ’yan sanda na tsawon shekara 14, bisa tuhumar zamba cikin aminci na Dala dubu 164. Sannan an harbe jami’in hukumar yaki da cin hanci da rashawa, inda aka yi masa mummunan rauni, don ya daina yi wa masu laifi kwarmato. Wannan mummunar  dabi’a ta jami’an gwamnati a Malawai, kafafen yada labarai sun yi amta lakabi da “Cashgate.”
Shugabar kasa, Joyce Banda ta bayyana wa ministocinta cewa “ba ta yarda da su ba,” don haka aka samu rudani a taron majalisar mulkin kasar.. Tusekele Mwanyongo, mai magana da yawun shugabar, ya bayyana cewa, an sauke ministocin kasar ne daga mukamansu don “a samu damar yin bincike a kansu.”
Shugaba Banda, wadda ta kasance daya daga cikin mata biyu da ke shugabanci a Afirka, ta kama ragamar mulki ne bayan mutuwar Bingu wa Mutharika a halin yanzu za ta fuskanci zabe a watan Mayun shekarar 2014. Sai dai tana da farin jinni saboda kokarin da take yi wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.