✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Badakalar Onnoghen: Kotu  ta yi watsi da bukatar Babban Jojin Najeriya

Onnoghen ne ya jawo takaddamar da ake yi – Farfesa Yadudu   Kotun Da’ar Ma’aikata (CCT) ta fara shirye-shiryen ci gaba da shari’ar Babban Jojin…

  • Onnoghen ne ya jawo takaddamar da ake yi – Farfesa Yadudu

 

Kotun Da’ar Ma’aikata (CCT) ta fara shirye-shiryen ci gaba da shari’ar Babban Jojin Najeriya Mai shari’a Welter Onnoghen da ake tuhuma da rashin bayyana kadarorinsa.

Wannan ya biyo bayan hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke ne a Abuja a shekaranjiya Laraba inda ta yi watsi da bukatar Babban Jojin na a hana Kotun Da’ar Ma’aikatan yi masa shari’a.

Kakakin Kotun CCT, Ibraheem Al-Hassan ya shaida wa wakilinmu cewa Alkalin Kotun CCT, Danladi Umar yana sane da hukuncin Kotun Daukaka Karar wanda yake nufin kotunsu ta ci gaba da shari’ar.

Sai dai ya ce har zuwa shekaranjiya Larabar kotun ba ta ajiye ranar da za a ci gaba da shari’ar ba, amma za a sanar da ranar nan gaba kadan.

A ranar Litinin da ta gabata ce Shugaban Kotun CCT ya dage zaman shari’ar har illa masha Allahu, don ba Kotun Daukaka Kara dama ta yi hukuncinta.

Badakalar Mai shari’a Onnoghen wadda ta jawo Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da shi a makon jiya ta jawo cece-ku-ce a ciki da wajen kasar nan.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP da Kungiyar Lauyoyi ta Kasa da wasu kungiyoyin kare hakkin jama’a sun yi tir da dakatar da Babban Jojin, inda suka bayyana hakan da kokarin danne bangaren shari’a da kuma yunkurin murde zaben tsakiyar wannan wata.

Sai dai Jam’iyyar APC a wata sanarwa a ranar Litinin ta nuna mamaki kan yadda Jam’iyyar PDP ta kidime saboda dakatar da Onnoghen, inda ta yi tambayar mene ne dalilin da ya sa PDP da dan takararta Atiku Abubakar suka shiga damuwa kan dakatar da Onnoghen, “Ko dai da walakin ne goro a miya,” inji ta.

Lokacin da Aminiya ta tuntubi farfesan shari’a da dokoki, Farfesa Auwalu Hamisu Yadudu game da takaddamar da ake yi kan dakatar da Babban Jojin, ya ce duk da cewa dakatarwar da Shugaban Kasa ya yi ga Babban Jojin Najeriya ba a yi ta kan ka’ida ba, amma ya kamata a fahimci cewa Babban Jojin ne ya fara karya doka.

“Tunda farko ya kamata mu fahimci abin da ya ja aka dakatar da shi din. Wannan mutum ne da yake matsayin mai yi wa mutane shari’a wanda har ya zama shugaban alkalan Kotun Koli amma a same shi da laifi. Laifin kuma ba wai kawai na kin bayyana dukiyar da ya mallaka ba har da boye ta tare da bin duk hanyoyin da ya ga zai iya wajen ganin ya tadiye shari’a ba ta yi aikinta a kansa ba. Rahotanni sn nuna yadda ya rika bin kotu daban-daban tare da janyo mutane iri-iri cikin lamarin don ganin cewa ba a gurfanar da shi gaban kotu ba. Idan a kasar da mutane suke da mutunci ne to da kamata ya yi ya ajiye mukaminsa bisa radin kansa kafin a kai ga dakatar da shi.  Don haka abin da Babban Jojin ya aikata abin a yi tir da shi ne. A matsayinsa na Shugaban masu shari’a wanda ya kamata ya bayar da misali amma ya lalata harkar shari’a gaba daya,” inji shi.

Farfesa Yadudu ya ce akwai matakan da ya kamata a bi kafin a dakatar da Babban Jojin wadanda kuma Majalisar Zatarwa ba ta bi su ba. “A dokance Shugaban Kasa ko Gwamna ba ya da hurumin ya dakatar da ko alkalin jiha ko na tarayya ballantana kuma Babban Jojin Kasa hakan ya hada da cewa ko da kotu ce ta bayar da wani umarnin yin hakan. Dokar cewa ta yi Hukumar Kula da Harkar Shari’a (NJC) ta nada kwamiti da zai yi bincike a kan zargin da ake yi wa alkalin kuma kwamitin zai mika tataccen rahotonsa gaban Shugaban Kasa da Majalisar Kasa kafin daukar mataki. Ba a bi matakan da aka tanada ba, an yi aiki ne kawai da umarnin kotu cewa a dakatar da Babban Jojin tare da nada wanda yake bin sa a mukamin rikon kwarya. Idan mun duba Babban Jojin shi ya jawo haka domin bai bayar da damar a yi masa adalci ba ta hanyar bin matakan da ya kamata wajen dakatar da shi din,” inji Yadudu

Farfesa Yadudu ya ce Babban Jojin a da aka nada na rikon kwarya babu wani laifin da ya aikata bisa karbar tayin mukamin da Gwamnati Tarayya ta yi masa, sabanin yadda Kungiyar Lauyoyi ta Kasa ta zarge shi da aikatawa. “Idan muka duba shi sabon jojin yana cikin tsaka-mai-wuya ba zai yiwu a matsayinsa na dan kasa ya ki karbar mukin ba saboda aikin bautar kasa ne. Ya kamata a yi masa adalci cewa ba shi ne ya nemi mukamin ba. Duk kuwa da cewa ba a bi ka’idojin da suka kamata wajen nada shi ba duk kuwa da cewa na rikon kwarya ne,” inji Yadudu.

Kungiyar ’yan takarar Shugaban Kasa a karkashin dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APDA, Alhaji Mohammed Shittu ta goyi bayan dakatarwar da aka yi wa Mai shari’a Onnghen inda ta ce Shugaba Buhari ya yi shi a lokacin da ya dace.

Alhaji Shittu ya ce a bisa fassarar doka Shugaban Kasa yana iya dakatar da duk wani ma’aikacin gwamnati da ake tuhuma da aikata ba daidai ba.