✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Badalaƙar ma’aikatan Zamfara

Ko shakka babu ba mu yi mamaki ba, akan waɗannan ma’aikatan gwamnatin bogi da gwamnatin Jjihar Zamfara ta bankaɗo, karkashin jagorancin sabon kwamishinan kuɗi, musamman…

Ko shakka babu ba mu yi mamaki ba, akan waɗannan ma’aikatan gwamnatin bogi da gwamnatin Jjihar Zamfara ta bankaɗo, karkashin jagorancin sabon kwamishinan kuɗi, musamman yadda kwamitin binciken ya bankaɗo wasu ma’aikatan bogi dake amsar albashi sama da daya. Sai kuma wasu da suke amsar albashi da sunayen wasu a bankuna daban-daban a jihar, wannan wani babban abin takaici ne da tir da Allah waddai.

Idan dai har wannan lamari ya kasance gaskiya hakika an cutar da mutanen Jihar Zamfara musamman talakawa masu rayuwar hannu baka hannu kwarya. Idan muka yi la’akari da ƙananan ma’aikata musamman na kananan hukumomi kasancewar wasu albashinsu ko cefane ba ya isarsu, amma ga wasu a gefe daya suna kwasar manyan kuɗaɗe babu wani dalili kwakwara, babban abin damuwa ma shi ne wasu daga cikin mutanen da wannan bincike ya banƙado suna amfani da sunan Hausawa a asusun ajiyarsu suna karɓar kuɗi alhali a fili suna amfanin da sunan da ba na Hausawa ba.

Muna kira da babbar murya ga gwamnatin Jihar Zamfara ta kara matsa kaini domin binciken irin wannan badaƙala don ya kasance an tantance ma’aikatan da ke aiki ne kawai suke karɓar albashi. Sai dai wani hanzari ba guba ba, mutanen da aka aza ma nauyin wannan bincike su yi aikinsu tsakani da Allah a bisa gaskiya, kar a yi kallon wannan dan jam’iyyar adawa ne, ko wani abu na daban.

Dukkan wanda aka kama yana karɓar kudade ta haramtacciyar hanya, muna fatan hukuma za ta yanke masa hukunci daidai da abin da ya aikata domin wannan babban zalunci ne, kuma cin amanar arzikin jiha ne, idan muka dubi ɗimbin al’ummar dake zaune babu aikin yi. A karshe ina addu’ar Allah Ya kawo mana zaman lafiya da arziki maI yawa.

Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau ɗan kungiyar muryar talaka ta ƙasa rashen Jihar Zamfara (08133376020)