Da Dumi Dumi

Badi nake sa ran sayen Arsenal – Dangote

Dangote
Dangote

Attajirin Afirka Alhaji Aliko Dangote, ya sake bayyana niyyarsa ta sayen kungiyar kwallon kafa ta Arsenal. Dangote, wanda ya sha bayyna niyyarsa ta sayen kungiyar ta Gunners a shekara biyar da suka gabata, cewa yana shirin sayen kungiyar shi ne na 96 a jerin sunayen mutanen da suka fi kudi a duniya, kamar yadda mujallar Bloomberg ta bayyana. Ya fara harkar kasuwanci ce tun yana dan shekara 21 wanda haka ya sa yake kan gaba a harkar siminti a Afirka, kuma a shekarar 2018 ya ce burinsa shi ne ya sayi kungiyar ta birnin Landan bana.

“Za mu sa kai a Arsenal nan da 2020… koda kuwa wani ya riga ni saye zan dai saya daga gare shi,” ya taba fada wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters a 2018. Yanzu kuma da ya sanya kai wajen aikin gina matatar mai a garin Legas da ake sa ran za ta zamo mafi girma a duniya, saboda yadda ake samun kwan- gaba-kwan-baya ga aikin, yanzu ana sa ran kammala ta a 2021, da hakan ya sa Dangote ya ce sai bayan ya gama gina matatar zai koma kan batun sayen Arsenal. Dangote wanda mujallar Bloomberg ta ce yana da kudin da suka kai Dala biliyan 14.1- ya kara tabbatar da cewa yana nan kan bakarsa ta sayen kungiyar mai buga gasar Firimiya ta Ingila. “Kungiya ce da tabbas nake sa ran saye wata rana, amma abin da a kullum nake fada shi ne a yanzu mun dauko aikin da zai lashe Dala biliyan 20 kuma shi ne a halin yanzu muka karkata a kansa.

“Ina kokarin in gama gina wannan matata, daga nan kuma nan da zuwa 2021za mu iya saye.

“Ba zan sayi Arsenal a yanzu ba, zan saye ta ce bayan na kammala ayyukan domin ina son matatar ta kasance ta kai mataki na gaba…”

Sai dai mamallakin Arsenal Mista Stan Kroenke, ya yi watsi da da’awar Dangote, inda ya ce tayin nasa ba abu ne mai yiwuwa ba.

ADVERTISEMENT

Jaridar Sportmail ta Ingila ta ce, lura da matsayin Stan Kroenke babu alamar zai iya sake jarinsa a kungiyar ga wani dan kasuwa a halin yanzu.

Share