Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Bai dace ba wani ya fito a matsayin Annabi Muhammadu ba a fim-Malaman addinai

Jagororin Cibiyar haxin kai da fahimtar Addinai Imam Muhammad ashafa da Fasto James Mavel Wuye sun gargaxi masu shirya fina-finai da ka da su tava sanya wani xan was an fim ya fito a matsayin Annabi Muhammadu a cikin fim. Da yake Magana a wajen wani taron horaswa na kwanaki biyar da aka shiryawa Ýan fim akan yadda za su yi amfani da sanaársu ta Fim don wayar da kan jamaá akan muhimmancin zaman lafiya wanda  Centre for Change and Community Development ta shirya tare da haxin gwiwar Institute for Peace and Conflict Resolution. Imam Ashafa ya ja kunnen masu shirya Fina-fina su guji yin duk wani abu da zai zubar da martabarsu da sanaársu ga idon jamaá. Musamman ta yin takatsantsan ga abin da ya shafi addinai da aládu da kuma tarbiyyar alúmma.

Imam Ashafa ya ci gaba da cewa “laifi ne babba a addinin Musulunci wani ya fito a matsayin Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a cikin Fim ko wasan-kwaikwayo. Haka kuma laifi ne babba wani ya zana surar Annabin ko ta wace siga. Don haka ina kira gare ku ka da ku yi abin da ka iya jefa masu kallonku cikin fitina.”

ADVERTISEMENT

Da yake nasa jawabin Fasto James Mavel Wuye cewa ya yi kamata ya yi duk wani wanda ya tashi shirya Fim ya yi kyakkyawan nazari akan abin da zai yi fim xin. Fasto Wuye ya ci gaba da cewa “Kirista na kwarai shi ne wanda yake girmama abin da wasu da ba kirista ba suka yi imani da dashi. Don haka bai yiwuwa misali kana Kirista kana son ka shirya Fim akan wani addini da ba naka ba, kawai ka zauna gida ka fara shirya shi. Ya zama wajibi ka yi nazari mai zurfi tare tuntuvar masana. Wannan ya zama tilas idan dai muna so mu kauce ma haddasa faxace-faxacen addini da na qabilanci.”

Taron horaswar mai taken ‘Fina-finan Hausa don kawo zama lafiya’ an shirya shi ne don bada horo ga masu shirya Fina-fina da jaruman fim ta yadda za su rinqa amfani da basirar da Allah ya basu wajen isar da saqo ga masu kallonsu akan muhimmancin zama lafiya a qasa baki xaya.

ADVERTISEMENT

Da yake jawabi shugaban qungiya mai zaman kanta wacce ta shirya wannan taro, Zack Amata ya jaddada muhimmanci yin amfani da Fim don qara haxa kan alúmma. A cewarsa “lokaci ya yi da masu shirya Fina-fina musamman na Hausa su juya akalar manufofinsu da saqonnin da suke aikawa ga jamaá, duba da cewa Arewacin Najeriya yana fuskantar qalubale na tsaro wanda ya shafi faxace-faxace na qabilanci da kuma addinanci.”

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa wani mahalaccin wannan taro kuma xan was an Fim Malam Musa Kalla cewa ya yi wannan taro ya zo daidai lokacin da ake buqatarsa ganin yadda ake samun rashin jituwa a tsakanin alúmmomi da daman a Arewacin Najeriya wanda kuma mafi yawa abubuwa ne qalilan ke taso da su waxanda zaá iya wayar da kan jamaá ta hanyar Fim akan qaurace masu.

Wata Ýar was an Fim da ta halacci taron daga Kaduna Malama Zainab Baka, ta nuna gamsuwarta da irin abubuwan da ake koya masu  wajen wannan horo, wanda ta ce zai taimaka masu matuqa wajen sake tunani akan ayyukan da suke gudanarwa.