✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bai dace ba yin sulhu da miyagun barayi – Barista Attahiru

A daidai lokacin da wadansu ’yan Najeriya ke ganin tattaunawa tare da yin sulhu da masu tada zaune-tsaye ne mafita wajen magance matsalolin da ke…

A daidai lokacin da wadansu ’yan Najeriya ke ganin tattaunawa tare da yin sulhu da masu tada zaune-tsaye ne mafita wajen magance matsalolin da ke addabar wasu jihohin kasar nan ba, Barista Attahiru Usman ya ce, abin da ya fi dacewa shi ne gwamnati ta yi amfani da karfinta a matsayinta na hukuma domin kawar da batagari tare da karfafa tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, ta hanyar yin amfani da dukiyar a kara sama wa jami’an tsaro kayayyakin aiki domin su samu damar yin aikinsu yadda ya dace. Lauyan ya ce a duk duniya babu inda ake sulhu da barawo wanda ya aikata barna.

“Mun gamsu da matakan da gwamnati ke dauka na dakile matsalar tsaro kuma wajibi ne al’umma su dafa wa gwamnati a wannan yunkuri. Kamar yadda yake alhakin gwamnati ne samar da tsaro su ma al’umma suna da alhakin taimaka wa gwamnati da muhimman bayanai domin sai al’umma sun bai wa jami’an tsaro hadin kai sannan za su samu damar yin aikinsu yadda ya dace. Amma maganar yin sulhu da barawo tare da yi masa afuwa ba na goyon bayan haka domin babu inda ake yin haka a duniya, ana yin sulhu ko afuwa ne ga wadanda suka tada hargitsi domin neman wani muradi nasu ko kwatar wa kansu wani hakki da suke hankoron an tauye musu. Amma ba a yin sulhu da wanda ya shiga gidanka ya yi maka sata ya zubar da jinin al’umma da sunan satar masu dukiya ko makamancin haka. A irin wannan kamata ya yi gwamnati ta yi amfani da karfinta domin magance hakan,” inji shi.

Barista Attahiru Usman ya bayyana haka ne a ranar Asabar da ta gabata lokacin da yake amsa tambayoyin ’yan jarida a taron addu’a da Kungiyar Kastinawa da Daurawa suka shirya a Jihar Legas.

Ya ce, wajibi ne jama’ar gari su rika hada gwiwa da jami’an tsaro domin cimma dawamammen zaman lafiya.