Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Bai dace matasa su rika cin zarafin shugabanni ta Intanet ba – Gwamna Udom

Gwamnan Jihar Akwa Ibom Udom-Emmanuel

Bai dace matasa su rika cin zarafin shugabanni ta Intanet ba – Gwamna Udom

Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Mista Udom Emmanuel ya gargadi matasa masu amfani da kafafen sada zumunta na zamani suna cin zarafin shugabanni, inda ya ce ya lura wadansu matasa na fakewa da kafafen sada zumunta suna cin mutuncin shugabanninsu.

Gwamnan ya fadi haka ne lokacin da ya gana da wadansu matasa masu kaunar ci gaban jihar a Uyo.

Gwamna Emmanuel, ya ce, “Na lura wadansu matasa daga cikin matasan jihar nan na fakewa da kafafen sada zumunta na zamani suna cin zarafin manyan ’yan siyasar jihar nan da kuma masu rike da mukaman siyasa wannan ya nuna karara masu wannan hali ba su da tarbiyya,” inji shi.

Daga nan Gwamnan ya bukaci iyayen yara su sa kaimi wajen sanya ido kan halaye da take-taken ’ya’yansu domin gwamnati ba za ta ci gaba da lamuntar irin wannan mummunar dabi’a ta cin zarafin jama’a ko rashin mutunta na gaba ba.

Ya dora alhakin hakan kan rashin ba yara tarbiyya da wadansu iyaye ke yi, inda hakan ya sanya kowa ke yin abin da ya ga dama.

Gwamna Udom, ya bukaci matasan jihar su zama masu ladabi da biyayya ga shugabanni, a cewarsa cin zarafin kowane mutum ba dabi’a tagari ba ce.