✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bai kamata a kirkiri sabbin masarautun ba – Sheikh Dahiru Bauchi

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya shawarci Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje kan ya guji yin duk wani abin da zai raba Masaautar Kano.…

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya shawarci Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje kan ya guji yin duk wani abin da zai raba Masaautar Kano.

Malamin ya bada shawarar ce a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a shekaranjiya Larabar a Bauchi.

“Muna jawo hankalin Gwmna Ganduje cewa ya yi wa Allah Ya kuma tsare mu daga fitina a kan Masarautar Kano. Mun ji cewan yana kokarn sake raba wannan masarauta bayan kotu ta soke. To ya kamata ya sani taba Fadar Kano ba wai iya Kano abin zai shafa ba, dukkan Musulmi ne musamman Tijjanawa, ya sani mu ’yan Tijjaniyya duk inda muke muna tare da Fadar Kano, ita ce ta yi dalilin zuwan Shehu Ibrahim Niasse Najeriya, sa’annan muna da yawa.”

Malamin ya ce masarautar Kano tafi shekara dubu kuma an yi gwamnatoci da dama, inda ya ce Bature ya zo ya yi shegantakarsa ya tafi bai taba masarautar ba, “muna jan hankalin gwamnan da ya tuna cewa kowa yana da burin a ce ya gama lafiya, kar ya taba masarautar don mu ’yan Tijjamiyya dukkanmu muna tare da Masarautar Kano da Mai martaba Sarkin Kano, Kuma muna da addu’o’i.”