Daily Trust Aminiya - Bai kamata a sanya siyasa a harkar ilimi ba – Farfesa Yakasa
Subscribe

Bai kamata a sanya siyasa a harkar ilimi ba – Farfesa Yakasai

Farfesa Salisu Ahmad YakasaiFarfesa Salisu Ahmad Yakasai shi ne Shugabab Sashin Nazarin Harsunan Najeriya a Jami’ar Usman dan Fodiyo da ke Sakkwato, wakilinmu ya tattauna da fitaccen a kan abubuwan da suka shafi ilimi a kasar nan:

Ilimi a kasar nan ci baya yake samu ko ci gaba ganin yadda jami’o’i ke yawaita a kasar nan?

Hausawa na cewa ba fankan-fankan ne kilishi ba tsomi ne, abin lura a nan, matakai daban-daban ya dace a ce ana tafiyar da su kan tsari. Kamar yadda muka sani ilimin jami’a shi ne mataki mafi girma da daukaka da kowane dan Adam yake son cimmawa, kuma kowace kasa da take son ci gaba takan yi kokari ta ga ta kafa jama’arta a wannan mataki, saboda a wannan bigiren nazari ne ake yin kowane bincike da zai kawo bunkasar al’umma da kasa baki daya. To, amma idan ya zamo an rasa tsari mai kyau bude jami’o’in kawai ake yi, to za ka samu akwai matsaloli manya. Idan ka lura abin da ke faruwa a Najeriya a gefen ilimi, siyasa ce ake gudanarwa ba harkar ilimin tsantsa ba. Lamarin ilimi ya fi gaban wasa, ba abu ne da za a yi sako-sako da shi ba, a rika bude makarantu yadda aka ga dama kawai saboda a rika fadin a lokacin wane an bude jami’a kaza ba don za a kula da ita, a kawo canji mai ma’ana tsakanin mutane ba, bai kamata ba. Misali a kowace jiha a kasar nan kusan akwai jami’a ta Gwamnatin Tarayya, kuma sai wasu gwamnoni suka yi karambanin kara bude jami’o’i mallakar jihohin. Abin lura a nan wasunsu ba su nazarci abin da kyau ba, mun san akwai tarin jama’a, amma bai isa ya zama dalilin yin gine-ginen ba tun da ilimin jama’ar bai ginu da kyau ba, kamata ya yi a inganta ilimin yaran a makarantun da ke gare mu kafin shigowa da wasu a kuma kyautata tare da duban matsalolin da ke addabarsu. Amma ina ba a duban wannan a kasar nan, kan haka yawaita bude jami’o’i mallakar jihohi ci baya zai kawo wa ilimi a kasar nan. A yanzu da nake yi maka magana ba wata jami’a a kasar nan da ke da isassun malamai da za ta iya alfahari tana da malamai dari bisa dari, babu. Kayan aiki da littattafai ba su ishe mu ba, a yanzu kuma zamani ya zo da wasu na’urori masu saukin sarrafawa domin neman ilimi a cikinsu da bunkasa shi, amma ba mu da su, har yanzu rarrafe ake yi domin a samu. Kudin da ake kashewa don gina wasu jami’o’i da wadanda muke da su ake ingantawa da ilimi ya bunkasa, amma yanzu Allah Ya kawo mana dauki. dauki jami’ar da aka gina a nan Sakkwato ga ta dan Fodiyo duk a cikin garin da mutanen Sakkwato da Zamfara da Kebbi da Katsina da sauran jihohi ke amfana da ita. Kudin da aka kashe domin gina sabuwar mallakar jiha da a dan Fodiyo aka sanya su suka bude sababbin kwasa-kwasai, wadanda ake da su aka ingata su da ya fi. Jami’o’in Gwamnatin Tarayya suna fama da rashin kudi da kula, sai ga shi an yi masu kishiyoyi da za su rika sha a kwarya daya, shi ya sa za ka rika ganin jiya ta fi yau, yau kuma ta fi gobe ka ga wadannan matsaloli ne. Kuma akan samu wasu gwamnoni da suke bude jami’o’in jihohi  da kyakkyawar niyya amma in aka yi rashin sa’a Gwamnan ya wuce, tana iya mutuwa, don kowane mutum akwai abin da yake son ya ba da karfi, hakan ya faru a Kudancin kasar nan. A ra’ayina jami’o’in da ake kirkirowa a jihohi an yi sauri, don ko wadanda muke da su an kasa inganta su, domin inda saniyar gaba ta sha ruwa ta baya ma nan za ta sha. Abin takaici karantu abu ne mai muhimmanci, amma an daina ba shi muhimmanci, sai mutum ya rasa aiki sai ya ce a ba shi koda malanta ce. Ya kamata mu dauki abin da muhimmaci don shi ne kafa ko sillar kowane ci gaba na kasa, duk kasar da ka ji ana tinkaho da ita, to, ta samu ci gabanta ne ta hanyar ilimi, don haka ya kamata mu cire siyasa a harkar iliminmu, ba abin boyo ba ne kowa ya san akwai matsala a cikin jami’o’inmu.  

Wadanne abubuwa kake ganin sai sun samu kafin a kafa wata jami’a?
Ya kamata a yi la’akari da wasu muhimman abubuwa kafin a bude jami’a, kamar malamai da kayan aiki ingantattu, a yi la’akari da lokacin ya dace da sauransu. Duk wadannan ya dace a tanade su kafin a soma bude makaranta ba jami’a kawai ba.  Misali akwai malaman ko babu? Duk inda babu a nemo su, bayan an samu a tanadar musu horo na sanin makama da kayan aiki don su rika aikin da kyau, kwalliya ta biya kudin sabulu, sa’annan a rika kyautata musu ta yadda ba za su rika barin aikin malanta suna komawa wani bangare ba. A samar da kayan aiki na zamani ba na dauri da ake amfani da su yanzu a cikin jami’o’inmu ba.

Wane irin tasiri kake gani ga ilimi mata musamman wadanda ke zuwa jami’o’i?
Abin da ya kamata mu duba shi dai ilimi nemansa abu ne mai fa’ida kwarai da gaske ga kowa, kamar yadda muka sani. Bahaushiyar al’ada; al’ada ce Musulma, kuma Allah Ya ba da damar a nemi ilimi, shi neman ilimi wajibi ne, a kan kowane Musulmi ba a ware aka ce maza kawai ko mata kawai ba, don haka ilimi na da matukar muhimmanci mata su neme shi, kamar yadda tsarin zamantakewarmu yake. Ilimi na kowa da kowa ne, saboda akwai abubuwan da ya kamata mata su yi wa mata ’yan uwansu kamar jinya da koyarwa da likitanci. Rashin samun haka na iya sanyawa ka ga wanda ba Musulmi ba ko namiji ya na duba mace Musulma, hakan ya sa ilimi ba ya da shamaki ga kowa. A yanzu an samu ci gaba sosai amma ana bukatar kari, wajibi ne iyayenmu su bar ’yan uwanmu mata su nemi ilimi daidai gwargwado na kowane irin mataki don za su yi wa al’ummarmu amfani da fa’ida, in ko ba su samu ba, za a bar mu a baya. Da iyaye da mazaje da gwamnati ya kamata mu taimaka wa mata su rika karatu gwargwado na addini da na zamani don Allah Shi ne ke da zamani. Akwai abubuwa da malamanmu ke ganin ba su da kyau, to, in mun shiga cikinsu ne sa’annan muke iya gyarawa. Da zarar ba mu shiga, za a bar mu a baya kuma gyaran ba zai zo ba, har yanzu kason da ake bukata ba a samu ba. Muna bukatar mata su wakilce mu a wasu wurare, ya dace a rika barin su suna karatu mai zurfi kamar aikin lauya da sauransu, idan ba mu bari namu suka yi ba, wadanda ba namu ba su ne za su yi. Kudancin kasar sun yi mana fintinkau saboda ba su da shamaki ga wanda zai nemi ilimi kuma sukan zo ne har wannan gefen namu don yin karatu. In har za mu kyale wasu ’yan uwa mata su yi ilimi kuma mu ne za mu koyar da su,ban ga dalilin da za mu hana wa namu ba, karatu wajibi ne in har akwai wasu abubuwa da za su yi linzami ko jagoranci na addini ko al’ada, ya kamata a kula da su wurin ilimin ba hanawa ba

A wannan lokacin ilimi ya yawaita amma ba ya da tasiri me kake ganin ya jawo haka?

To, a nan abin da yake kawo matsalar shi ne kowa so yake ya samu suna don ba a yin abin da kyakkyawar niyya, saboda haka manufar ce ba ta da kyau, in da ana kyautata niyya ga duk abin da za a yi, to, sai mu ce wannan abin an assasa shi ga hanya mai kyau, duk abin da ya shafi rayuwa in ba a yi yadda ya kamata ba, to, ba za a samu tasiri ba. Yanzu ga shi ana samun yawaitar masu takardar shaidar karatu  da yawa, amma ilimin ba ya da nagarta, wannan babbar matsala ce, matukar niyya ba ta inganta ba matsalar ba za ta kau ba, duk abin da za a yi sai ya zama suna kawai kuma ba a iya komai ba. Duk wanda ya yi dubi da idon basira zai ga yanzu mun kasance kara-zube kowa yana yin yadda ya ga dama, kowa ta kansa yake yi, maimakon mu rika tafiya daidaiku ya kamata a rika ganinmu a dunkule a al’ummance don amfaninmu, don dunkulewar al’umma ita ce ginshiki na tafiyar da rayuwa.

Harshen Hausa yana bunkasa amma Hausawa na ci baya, me za ka ce kan haka?
Gaskiya ne harshen Hausa yana ci gaba, in ko aka ce harshe yana bunkasa, to, shi ne ya nuna al’ummar harshen na ci gaba. Illa abin da ya kamata a ce shi ne al’ummar da harshen suna bukatar kulawa fiye da yadda suke da ita a yanzu. Saboda duk da harshen yana bunkasa wasu mutane da ba Hausawa ba ne ke kokarin ciyar da harshen a gaba, wurin gina shi da raya al’adunsa. Akwai bukatar Hausawa su rungumi harshensu da kyau wurin yada rassan harshen guda uku wato adabi da harshe da al’ada. Akwai bukatar kara gina su don su samu karbuwa ta hanyar rubuce-rubuce ko mutane su iya bayyana kansu. Wajibi ne a samar da sha’awar harshen a cikin al’umma, ba wani abu na rayuwa da zai samu nasara ba tare da harshe ba, don haka harshe da al’ada tare suke tafiya. Muna bukatar a ba da himma domin ba wani mutum da zai zo ya yi maka abu, kuma naka ne koda zai yi ba zai yi kamar ka ba, kai da ka mallake shi. Har wa yau akwai bukatar himmatuwa wurin gane ilimin kimiyya wanda a al’adar Bahaushe babu shi don a yanzu shi ne ginshikin ci gaban kowace al’umma, kuma mu Hausawa ba za a bar mu a baya ba. Harshe kamar mutum ne yana mutuwa, don haka ya kamata mu kara azama, don ganin an kara samun bunkasar wannan harshe yadda zai dore matukar akwai al’ummar Hausawa don ciyar da harshe gaba.

texem
More Stories