Da Dumi Dumi

Bai kamata gwamnati ta yi sulhu da ’yan ta’adda ba – Miyetti Allah

Jama’a a yayin taron sulhu da ‘yan bindiga a fadar Sarkin Gummi, a Jihar Zamfara kwanakin baya
Jama’a a yayin taron sulhu da ‘yan bindiga a fadar Sarkin Gummi, a Jihar Zamfara kwanakin baya

Sakataren Kungiyar Miyetti Allah  Kautal Hore ta Jihar Bauchi Alhaji Sadik Ibrahim Ahmed ya ce duk Bafulatanin da ya aikata laifi aka kama shi, a daure shi, a yanke masu duk hukuncin da doka ta tanada gare shi.

Sadik ya yi wannan kalami ne lokacin da yake amsa tambayoyin wakilinmu dangane da sulhu da ake yi da mahara.

“A gaskiya batun sulhu da ake yi, mu Fulani ba ra’ayinmu ba ne, don muna da kunya, aikata laifi abin kyama ne a wajenmu. Ban san yadda ake zama da na sama da mu ba a matakin tarayya amma ni a ra’ayina, bai kamata gwamnati ta ce za ta yi sulhu da ’yan ta’adda ba; wannan gazawa ce a bangarenta. Duk Bafulatanin da aka same shi ya aikata fashi da makami, ya kamata a hukunta shi kamar yadda dokar kasa ta ce amma ba a ce za a yi sulhu da shi ba,” inji shi.

Ya ce “Mu Fulani, Allah Ya ba mu kunya da basira da komai aka ba mu horo a kai, za mu iya saboda basirarmu don haka a yau abin da yake faruwa, wadansu ne ke sa Fulani cikin wannan harka ta fashi da makami da yin sata da garkuwa da mutane da satar shanu. Bafulatani bai san komai ba sai shanunsa, an hana shi kasar kiwo, an hana shi hanyar da shanunsa za su bi su yi kiwo; kai hatta da rani gwamnati ta kawo noman rani, kamar yadda kwalta ta cinye labin shanu, haka noman rani ya cinye fadamun da Bafulatani ke kiwo. An sace shanunsa, don haka idan ya rasa shanu wani ya ja hannunsa zuwa aikin assha sai ka ga ya dauka kuma ya kware a kai. Kalilan da ake samu su ke aikata laifuffukan kamar yadda sauran kabilun ke aikatawa, don kowace kabila ba a rasa mutanen banza, sai a daure su a yi musu hukunci ko hukuncin kisa ne in ya kama a yi musu. Mu wannan shi ne sakamako daidai da aikin da suka aikata.”

Sakataren ya ce “A matsayin kungiya, a kullum muna wayar da kan Fulaninmu su bi dokoki kada su shiga cikin masu aikata laifuffuka kuma su guji wadanda ba su sani ba, su ja hannayensu su sanya su cikin aikata miyagun ayyuka kuma idan gwamnati tana so a shawo kan wannan matsala, tilas sai an yi wa Fulani adalci; a samar musu da tsaron dabbobinsa, a samar musu da dajin kiwo, a samar musu da labin ashanu da mashayar ruwan shanu. In an yi haka za a samu zaman lafiya.”

ADVERTISEMENT
Share