✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bai kamata Kungiyar CAN ta tsoma baki kan zaben shugabannin majalisa ba – Jama’atu 

Babban Sakataren Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta Kasa, Dokta Khalid Abubakar Aliyu ya ce bai kamata Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta ce a raba…

Babban Sakataren Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta Kasa, Dokta Khalid Abubakar Aliyu ya ce bai kamata Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta ce a raba shugabancin majalisa a tsakanin Musulmi da Kirista, inda ya tunatar da ita cewa wanda bai yi shuka ba ba ya zuwa ya ce zai yi girbi.

Sheikh Khalid Abubakar Aliyu ya bayyana haka ne lokacin da yake mayar da martani kan bukatar da Kungiyar CAN ta gabatar ta a ba Kirista shugabancin Majalisar Dattawa ko ta Wakilai, ya ce Jama’atu Nasril Islam tana tunatar da CAN da sauran ‘yan Najeriya cewa lokacin mulkin Goodluckl Jonathan shugaban Majalisar Dattawa Kirista ne wato Sanata Dabid Mark, Mataimakinsa Ike Ekweremadu ma Kirista ne.

“Sannan Shugaban Masu Rinjaye a majalisar shi ma Kirista ne. Shin a lokacin an ji Musulmi na korafin cewa dole sai ya zama Musulmi. Amma su sun saba irin wannan korafi. Domin a sanin Jama’atu Nasril Islam ’yan siyasa kansu ba su gama hadewa ba a kan wa za su zaba amma da yake CAN sun saba shirin bayan fage domin da su ake shirya abubuwa, ba’a shiryawa da mu shi ya sa yanzu kila suka ga in an gama shiryawa Musulmi ne zai zama, shi ya sa suke wannan kuka,” inji shi.

Dokta Khalid Aliyu ya ce “Idan shugabannin Kungiyar CAN suka ci gaba da yin haka ba zai haifar mana da mai ido ba, mu Jama’atu tsakaninmu da harkar ’yan siyasa iyakaci mu ba su shawara.Ba mu shiga harkar siyasarsu. Saboda su ’yan siyasa cewa suke da kowa suke tafiya shi ya sa dole mu sa ido, fatarmu kasarmu ta zauna lafiya, a yi ayyukan da za su kawo mana ci gaba da zaman lafiya mu samu damar yin addininmu. Domin idan babu zaman lafiya babu yadda za a samu kwanciyar hankalin yin addini yadda ya kamata.”

Babban Sakataren Jama’atu ya ce, “Lokacin mulkin Shugaba Jonathan Shugaban Kasa Kirista ne, Shugaban Majalisar Dattawa Kirista ne Sakataren Gwamnatin Tarayya Kirista ne. Ba cewa muke yi shi ma ya yi daidai ba ne amma abin da muke cewa shi ne ba mu yi korafi ba. Don haka su bar wa ’yan siyasa harkarsu domin su kansu ’yan siyasa ba su gama daidatawa ba har yanzu kokari suke yi su ga wane yanki za a bai wa.  Su kansu ’yan siyasa ba su san tsari ba, idan an yi tsari sai su dakile tsarin domin biyan bukatarsu wanda hakan ke janyo tashin hankali a tsakaninsu.”