Search
Subscribe
Bai kamata mutane su rikice saboda cutar Kurona ba – Sheikh Muhammad Sulaiman

Sheikh Muhammad Sulaiman Limamin Masallacin Sultan Bello Kaduna

Bai kamata mutane su rikice saboda cutar Kurona ba – Sheikh Muhammad Sulaiman

Sheikh Dokta Muhammad Sulaiman Abu Sulaiman shi ne Babban Limamin Masallacin Sultan Bello, da ke Kaduna. Kuma malami ne a Tsangayar Koyar da Addinin Musulunci a Jami’ar Jihar Kaduna. A  tattaunawa da wakilinmu, kan cutar Kurona da ke yaduwa yanzu a duniya, ya ce komawa ga Allah ne babban maganin cutar:

Me za ka ce game da annobar cutar Kurona da yanzu ake fama da ita a duniya?

Wadannan cututtuka da suke faruwa annoba ce. Kuma Allah Madaukakin Sarki Yana aiko da annoba ga al’ummar da ta fandare wa dokokinSa. A kowace kasa idan aka samu al’umma da barna ta yi yawa, sai Allah Ya jefa musu wata annoba.

Saboda Allah Madaukakin Sarki Yana cewa “Rundunar sojojin Ubangijinka, babu wanda ya san adadinsu, sai shi.” Don haka sai mu ga wata kasar rundunar da za a tura musu, ita ce girgizar kasa, wata kasar ambaliyar ruwa, wata kasar gobara, wata kasar kuma a tura musu cutar amai da gudawa.

Nana A’isha (RA) ta tambayi Manzon Allah (SAW) mece ce cutar annoba? Sai ya ce cutar annoba wata cuta ce da Allah Madaukakin Sarki Yake azabtar da bayinSa da ita, idan barna ta yi yawa.

To ka ga yanzu duniya ta rikice, ko’ina barna ake yi, an mayar da giya ta zama kunun zaki. Zina da luwadi sun zama ko’ina ana yi, wato maza su nemi maza, mata su nemi mata har dabbobi mutane suna nema yanzu.

Kuma idan ka koma bangaren cin amana da sata da zubar da jini, duk wadannan abubuwa suna jawo annoba. Idan ka koma ga mu’amala, a kowane bangare ana cutar juna. Ma’aikatan gwamnati suna cuta, ’yan kasuwa suna algush, manoma da ’yan makaranta da malaman makaranta, duk suna cuta. Wato idan ka dubi duniyar baki daya, kamar yadda Allah Madaukakin sSrki ne Yake bayyanawa, cewa: “Barna ta faru da yawa, a cikin kasa da ruwa da sararin samaniya.” Babu inda za ka je face sai ka samu barna.

Saboda haka Allah Yake aiko da annoba ko mutane za su gyaru, su dawo ga dokokin Allah.

Idan annoba irin wannan ta faru, ba ta ware wata kasa a duniya. A ce wannan kasar don ba kasar Musulmi ba ce, babu ruwanta ko kuma don wannan kasar Musulmi ce babu ruwanta.

Idan ka lura akwai annobar da Allah Ya jefa wa kasashen Musulmi. Ka fara tun daga kasar Afghanistan ran mutum miliyan nawa aka rasa, a kasar. Idan ka dawo kasashen Iraki da Libya da Siriya da Yemen da Sudan da Kudancin Sudan da sauran kasashe daban-daban na Musulmi, masifu sun fado masu. Kuma duk saboda kauce wa Allah ne da aka yi.

Saboda haka Allah Madaukakin Sarki Ya bayyana mana idan irin wannan annoba ta zo, tana gamewa ne ga kowa da kowa, kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Yake cewa “Ku ji tsoron fitina, idan fa ta zo ba za ta shafi wadanda suka jawo ta kawai ba.” Za ta hada kowa da kowa ne.

Saboda haka annoba tana zuwa ne bisa ga abin da hannayenmu na dama suka jawo mana. Don haka wajibi ne mu koma ga Allah mu ci gaba da rokonSa.

A nan Najeriya idan ka lura, wannan cuta ta Kurona da ta shigo, mutum daya ne aka ce ya shigo da ita. Kuma yanzu ana nan ana binciken duk mutanen da ya yi mu’amala da su. Saboda haka sai mu roki Allah Madaukakin Sarki, abin ya tsaya a haka.

Kuma Manzon Allah (SAW) yana ce mana idan annoba ta shafi gari, kada mutanen da suke cikin garin su fita, haka mutanen da ba sa cikin garin, kada su je su shiga wancan gari, haka Musulunci ya tsara. Don haka muke kira ga hukuma ta yi la’akari da cewa akwai wasu kasashe da muke mu’amala da su, kuma an tabbatar cewa wannan cuta ta shiga kasashen. Don haka mu’amalar da za mu yi da su a dakatar. A kula da filayen jiragenmu da tashoshin jiragen ruwa.

To mene ne mafita kan wannan al’amari?

To mafita  ita ce babu maganar tsoro, amma tsoro irin na al’ada wannan babu laifi. Amma mutum ya ji tsoron mutuwa, mutane su rikice suna tsoro wai kada su mutu. Mutuwa dai ba a sha mata kau-da- bara, abin da Allah Madaukakin Sarki Yake ce mana ka fada musu mutuwar da kuke gujewa lallai wannan mutuwa za ta zo ta same ku. Don haka mutum ya guje wa mutuwa, ba ta taso ba. Allah Madaukakin Sarki Yana bayyana mana ba zai yiwu ba, ga wani rai ya mutu, sai idan kwanansa ya kare. Saboda haka ban ga dalilin da zai sanya mutane su ji tsoron mutuwa ba domin kullum muna cikinta.

Idan kana jin tsoron cutar Kurona, to ai mu a nan kullum muna cikin cutar Kurona, tun shekara 11 da ta gabata. Tun daga cutar Boko Haram, wanda a kullum suna kashe mutane ga masu kai hare-hare ga masu garkuwa da mutane ga ’yan fashi da makami ga direbobi da suke mugun gudu suna hadarurruka. Mutane suna mutuwa, duk wadannan abubuwa annoba ce.

Don haka mafita ita ce mu koma ga Allah, mu roke Shi Ya yaye mana wannan annoba. Misali a lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba Ya da lafiya da Musulmin Najeriya da Kiristocin Najeriya har da wadanda ba su yarda da Allah ba, mun yi ta rokon Allah Madaukakin Sarki, kan Ya ba Shugaban Kasa lafiya  kuma Ya amshi addu’armu, Ya ba shi lafiya.

Saboda haka a yanzu ma sai mu tashi mu roki Allah, Ya yaye mana wannan annoba. Allah Ya ce ku yi ta rokon gafara, Allah zai gafarta muku zai saukar muku da ruwan sama, zai ba ku dukiya, Ya ba ku ’ya’ya masu lafiya da biyayya da tarbiyya, wannan shi ne mafita.

Sakamakon wannan annoba ta Kurona Kasar Saudiyya ta dakatar da zuwa kasar, don aikin Umara me za ka ce?

Gwamnatin Saudiyya ta yi hangen nesa kan wannan mataki da ta dauka. Domin idan ka lura duk duniya babu inda ake zuwa a taru, irin kasar Saudiyya. Mutanen da suke zuwa Umara Saudiyya daidai suke da mutanen da suke zuwa Aikin Hajji. Domin suna zuwa ne daga kasashe daban-daban. Don haka idan masu wannan cuta suka shigo kasar, za su hadu da sauran mutanen duniya. Domin za a hadu a masallaci da wajen cin abinci da wajen shiga motoci da jiragen sama. Kuma idan aka hadu da masu wannan cuta aka cakudu, ka ga zai kasance sun baza wannan cuta a kasar ta Saudiyya, kuma duk mutanen da suka zo daga sauran kasashen duniya idan suka koma, kasashensu cutar za ta dada bazuwa.

Ka ga ashe Saudiyya ba wai kasarta kadai ta kare ba, har da sauran kasashen duniya ta kare kan wannan mataki da ta dauka. Don haka muna tare da wannan mataki da kasar Saudiyya ta dauka, 100 bisa 100 domin shi ne koyarwar Manzon Allah (SAW) da yake cewa, idan annoba ta auku a gari, kada a bar wadanda suke cikin garin su fita, kuma kada a bar wadanda ba sa cikin garin su shigo. Kowa ya yi hakuri da abin da Allah Madaukakin Sarki Ya dora masa.

Kuma muna yaba wa Shugaban Hukumar Hajji ta Kasa kan sanarwar da ya bayar, na dakatar da karbar kudaden masu zuwa Umara, sakamakon wannan mataki da Saudiyya ta dauka, har sai an ga yadda al’amarin ya tsaya. Wannan abu da aka yi ya nuna kamar an yi adalci domin karbar kudaden mutane ba a san abin da za a yi ba, a je a yi ta juya musu kudadensu bai dace ba, don haka ya kamata a tsaya a yi la’akari, da wannan.

Kuma muna kira ga Gwamnatin Tarayya kan ta dauki irin wannan mataki ta hana shigo da duk wasu kayayyaki daga kasashen da suke fama da wannan annoba, kuma ta hana mutanensu shigowa, kuma a hana ’yan Najeriya zuwa wadancan kasashe.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin