✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bala mai son wasa

Assalamu alaikum Manyan Gobe tare da fatar ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Bala mai son wasa’. Labarin ya yi nuni…

Assalamu alaikum Manyan Gobe tare da fatar ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Bala mai son wasa’. Labarin ya yi nuni ne ga irin illar da yawan wasa ke janyo wa mutum. A sha karatu lafiya:

 

Bala yaro ne wanda yake son yin wasa sosai. Ga shi iyayensa marasa karfi ne. Mahaifinsa yana iya kokarinsa domin ganin  dansa ya samu ilimi mai inganci. Idan malamin Bala yana koyar da su a aji Bala hankalinsa na waje. Walau yana kallon  kadangaru ko tumaki masu wucewa. Hakan ya sa yake zama na karshe a ajinsu.

Saboda tsananin wasa in aka aike shi sayen wani abu yakan zubar da kudin ya koma gida yana muzurai. Mahaifiyarsa abin ya ishe ta sai ta shiga dukansa duk lokacin da ta aike shi ya zubar da kudi.

Bala ya kasance yaro dan shekara goma. Ran nan sai mahaifiyar ta ga ya yi fitsarin kwance. Ko da ta tambaye shi dalilin yin hakan sai ya ce mata ya yi mafarki suna cikin wasa ne shi ne ya yi fitsari.

Da mahaifinsa ya samu labarin sai shi ma ya shiga jibgar Bala.

Tare da fatar Manyan Gobe sun dauki darasi daga wannan labari.  Yawan wasa yakan sa yaro ya kangare sannan ya zama dakiki.