Search
Subscribe
Bala’in Bobon Bokokon Bara-gurbi (3)

Bala’in Bobon Bokokon Bara-gurbi (3)

Tsilla-tsillar tsuntsaye

Tsautsayin tsaye-tsaye

Tsokacin tsikarar tsinkaye

Tsomomuwar tsimin tsumaye

Tsatsubar tsunburbura ta tsiyaye

 

Bambamin bambance-bambance

Buyagin barace-barace

Carin ce-ce-ku-ce

Kwakwazon kwatance

Kakarin karance-karance

 

Rikon ragamar rubuce-rubuce

Zantukan zaman zaurance

Bakunan bakancen bakace

Sukuwar sukunin sakace-sakace

Sasarin sunkurun sammace

 

Dari-dari-da-dar-dar

Buruntun babatu-ka-batar

Watangaririyar wawa-ka-wurgar

Wowon wasan wuta ne-wautar

Wulkitawar wasa wukar

 

Kukuta-ka-kayatar

Karajin karamar kasar Katar

Kamuya-muya-ka-kaskantar

Kundunbalar kumbiya-kumbiya-ka-karatar

Kolo Kirkiri karar kararawar kar-kar

 

Takarkare-ka-tunatar

Fafata-ka-fadakar

Jajibe-jajibe-ka-jefar

Fito-ka-fahimtar

Karanta-ka-karantar

 

Lallai-ka-ladabtar

Ta’adi-ka-tunkudar

Zakuda-ka-zaburar

Amarya-an- aurar

Ango-aka-ankarar

 

Bin kadin batutuwa bambarakwai, na rai kwakwai, mutu kwakwai da suka yi wa kwakwalen dalbai kawanya, sun nunke su a baibai, har ta kai ga daukar rai nunke a baibai, tare da jikkatar jikkuna da tabbai, kamar yadda kafofin watsattsake da falle shafukan mujallu da makalu baje a jaridu suka wassafa wa al’umma a fadin duniya. Kodayake dai mu a Haurobiya an fi jiwo amon kassara rai a tsakanin masu koyon watsattsake da wangale wagagen littattafai da ke Kadadar Kudancin kasar, musamman a Jam’in Jama’ar Jami’ar In-yi-suka ko IN-SAUKA. Wannan ai shi ne SAKAKA SAKARCIN SAKACI SARAI-SARAI! SUNKURUN SASARIN SUKAR SAKARAI; WAUTAR WAWA WASARARAI! BIRGIMAR BIDIRIN BIRAI; TSINGARON TSAKUWAR TSANGWAMAR TSAYAYYUN TSIRRAI!

Watakila dawurwurin dumuiniyar darkake Dawai da baragadar bangaje Buwai da kishin kisisinar kishiyar kashe-kashe ba ta baibaye Arewatawa ba, saboda tuni suka yi wasararai da ran ’yan’yan ALARAMMAN ALMAJIRAN AREWATAWA, inda kolo da tittibiri da gargadin garada ke ta watangaririya a kwararo-kwararo, tunda an kasa yi musu MANHAJA MARA HAJIJIYA, yadda za su yi ninkaya da iyo a kogin ilmu, su yi takun BALAGURON BOBON BOKOKO, har su ji dadin kwankwadar koko. Kai Malam mai yaren Hau-hau wajen hawan sa ba tare sa-in-sa ba, ya ce SHAN KOKO BUKATAR RAI, shi ya sa ma a wani darasin wannan farfajiyar makarantar Dodorido, ni kuwa na ce a  A BA NI GASARA, ko ma ‘KAMU’ na kamen tabahuwar da ke tunkarar ’yan dugwi-dugwi, ’ya’yan Inna da Baba. Hasali ma dai, da ruwan tumbi ake jawo na kwakwaren burtsowar burtsatse.

Baje batutuwan bututun butun-butumin botoramin bambamin bilinbituwar balbalin bala’in banke baragurbi bai dace ba. Domin mafi yawan masu kawar da rayuwarsu a jam’in jama’ar jami’o’i sun samu hargitsin hasashen hasken harkallar hada-hadar hadurran haukacewar hankali. Ta yiwu ma suna cikin jerin wadanda suka yi: Dungun darussa da jan dagar darasin  dirasa a make-maken makekiyar  madarasa, ta mahangar motsa muka-mukin mamular masa a dabarbarcewar dawurwurin dumuiniyar dasisa, ta yadda a irin wannan yanayi suka kasa fasko cewa, ‘ akwai bukatar a bar kafa wa kai kusa, don ka da a karke da hana bodari yin tusa, saboda kawai ana son ganin matsaloli sun gurgusa, don jin dadin gantsarar gutsirar gurasa, wai fafutika ce dai ba a so a fasa, har a kai ga jan janjamin jimurdar Jarabar jarabawar  Jajibe-jajiben jibgewar jan Jibar jabgawar Jaye-jayen juye-juyen Jam’in jama’ar jami’ar Jamusawa, inda ake ta kundunbalar Kurmusun kamusun kadamusawa da Kwakume-kwakumen kwakumewar Kandare-kandaren kandarewar Kadandoniyar kwambon Kobarewar kundun kudundunewa.

Abin lura dai, shi ne, a harkar watsatsake a yi komai  keke-da-keke alkalami dai  ya zamto fekakke, don  sadarar tafiyar tsutsa ta kasance a mike. Ko a kauce wa make-make; har a samu masu koyi-ka-koyar  sun yi watsi da koyi-ka-karkatar ko koyi-ka-kayar don gudun dari-darin da yakan haifar, ballantana a dinga zaman dar-dar

’Yan makaranta ka da a shiga dawa, a nemi karuwa, ban da kwaruwa, ballantana a kai ga kassara rayuwa, ta yadda lullumin Lumana  kawarsa za ta zamo da ban sha’awa, har a zo ana kyakyatawa, al’umma na tafawa, kusan kowa na darawa.

Da zarar an kawar da FUSHIN FASHIN FACAKAR FINCIKAR FICIKA a tsakanin jiga-jigan jan ragamar al’umma, sai a samu dalibai zakakurai masu tarairayar rai, wadanda ba sa wasararai da rayuwa. Kuma jami’an jan ragamar jam’in jama’ar jami’o’i a daina nuna halayayyar nan ta jajibe-jajiben jibga jibar jafa’i da koyi-ka-karkatar, ko ma karkewa da koyi-ka-kayar. Su kuwa masu koyon watsattsake da wangale wagagen litattafai, wajibi ne su kiyayi shagalar shagulgulan shagalin shagirin shedancin sharholiyar shashanci sharandabar sharbar sholin shantakewar shan mandular moli. Sannan su kiyayi darsuwar dawainiyar dauke-dauken daukakkiyar tara dukiyar danniyar dumuiniyar dadin duniya. Rashin ji ke sanyawa a karke da BARAGADAR BUBBUGAR BAMBAMBAMIN BILINBITUWAR BALBALIN BALA’IN BOBON BOKOKON BARAGURBI; BULKARAR BURGAR BAGUN BUGA-BUGAR BUWAI; BASAJAN BAGARARWAR BASARWAR BUGUN BULALA; CARIN CANCAREWAR CARKIN CILKOWAR CAKWAIKWAIWA CAKWAI ko DABARBARUN DUMUINIYAR DABURCEWAR DAMFARAR DAMUN-FURAR DUMFARAR DARKAKE DAWAI; SHISSHIGIN SHASHANCIN SHEGANTAKAR SHAGALAR SHANTAKEWAR SHAWAI. Domin kwankwadar kwayoyi ko mulmula mandular moli da shagalar shantakewar shagalin shan sholi da mamungar mangare-mangare mamayar maye ‘baragada ce,’ kai waye. Lallai mu farka yau gari ya waye. Ka da mu bari a bijiro mana da tambaya, cewa, ‘yau wa gari ya waya?’

Dangane da bambamin bambance-bambance kan buyagin barace-barace, sai a bar carin ce-ce-ku-ce ko kwakwazon kwatance da Kakarin karance-karance. Abin yi dai kawai, a kyautata rikon ragamar rubuce-rubuce da zantukan zauren  zaman zaurance a bakunan bakancen bakace. Shi ke nan sai sukuwar sukunin sakace-sakace a warware  sasarin sunkurun samamen sammace.

Kuma a yasar da Dari-dari-da-dar-dar da Buruntun babatunbatarwar Watangaririyar wawayen wurgarwa a wautar wowon wasan wuta ko Wulkice-wulkice wasan wasa wuka. Domin da zarar an daba wa ciki carin carkin cakwaikwaiwa zai haifar da bakin ciki.

Matukar dai aka aka kyale shafaffu da mai suka ci gaba da RUMURMUTSAR RABASHEN RAGADADAR ROMON RAGON ROMOWA, ga GARARUMAR GARABASAR GIRKIN GIRKAWA, tare da SHARANDABAR SHARBAR SHARBEBIYAR SHAWARMAR SHIRWA SHIRU, alhali an yasar da ALARAMMOMIN AJAMAWAN AJAMIN ALKINTA ALLUNA ANA ARANGAMAR ARTABUN AIKA-AIKA AUKA musu, tabbas a sani mabiya ADDININ FUSKANTAR ALKIBLA DON KADAITA MAHALICCI DA IBADA za su fasko cewa su ake son kassarawa. Don haka sai a lalubo masu ruwa da tsaki, ta yadda ba za a ari bakunansu a ci musu ALBASHE-BASHE MAI LAUSHIN LAWASHI BA.

 

Haurobiyawa, mu yi wa kawunanmu masalaha, tunda bukatar bokokon bunkasa burgamen kasa ake hankoro, sai a yasar da baragurbi, a bi babi-babi da karatu bi-da-bi. Su kuwa masu dumuiniyar dandazon dankanzo, sai a kira su, su zo a nusar da su illar buyagin bilinbituwar barace-barace.

 

Domin ta haka ne kawai za a iya kauce wa tsilla-tsillar tsuntsayen tsautsayin tsaye-tsayen tsokacin tsikarar tsinkaye, ballantana tsomomuwar tsimin tsumaye da tsatsubar tsatsube-tsatsuben tsunburburar da ta tsiyaye.

 

Hukuncin a anan dai, shi ne, a takarkarewar tunatarwa da fafatawar fadakarwa, ta hanyar jefar da Jajibe-jajiben jibgin jiba; sai a  firfito a fahimtar. Kun ga ke nan, mai bobon bokoko ko Alaramman alaramomi sai ya Karanta-ya-karantar. Duk wanda ya tafka ta’asa a kwanon tasa, to ba wasa; lallai-a-ladabtar, sannan ta’adi-a-tunkudar tare da zakuwar zakudawar zaburarwa. Wannan sabuwar dabarar gyare-gyare wareware sasarin BALA’IN BOBON BOKOKO BARAGURBI  da JIMAMIN JIMURDAR JA-IN-JAR JIRKITA JAMA’A, musamman ’ya’yan ALARAMMAN ALMAJIRAN AREWATAWA sai ta zamto tamfar amarya ce aka aurar, shi kuwa ango aka nusar da shi, a ankarar, aka fadakar kan hakkoki; ka da a niki gari niki-niki, har ta haifar da tarnaki. Tsohon tsari ya yi toho,  ya fito da wani abu sabo. ’Ya’ya da iyaye da aka haifar, wajibi ne su ciyar, su tufatar, sui tarairayar a tarbiyantar, kun ga shi ke nan in an yi abin da ya dace babu wanda zai koka kan cewa ’ya’yan Inna da Baba an yi watsi da su tamfar ’ya’yan dabba, ko ma a ce sun karke da zama ’yan daba.

 

Haurobiyawa idan NA-ZOMO YA JI wannan batu, to GANGAR JIKI TA TSIRA. JIKI DAI MAGAYI BANKAR BUKIN DAN KORAU!

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin