✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Balarabiya tana sayar da sakarta don tara kudin tiyatar kyanwarta

Balarabiyar Hadadddiyar Daular Larabawa tana sayar da kayan sakar hannu don ta tara kudin yi wa magenta tiyata a asibitin dabbobi. Magen Fatma Sawas kanta…

Balarabiyar Hadadddiyar Daular Larabawa tana sayar da kayan sakar hannu don ta tara kudin yi wa magenta tiyata a asibitin dabbobi. Magen Fatma Sawas kanta ta kumbura, inda aka gano tana fama da ciwon hanta makonni uku da suka wuce, kuma dole sai an yi mata aiki, inda za a cusa mata mazurarin abinci kafin a kwantar da ita a asibiti.

Kudin maganin ya taru har ya kai Dirhami dubu biyar, tare da karin wan I Dirhami dubu uku da 600 na wani aikin da za a yi wa kyanwar.

“Magen mai lakabin BigHead ta cire mazurarin abincin da kanta, amma hoton sassan jikinta da aka dauka ya nuna cewa akwai wani abu a cikinta, wanda ke bukatar a yi mata aiki don fitar da shi,” a cewar Fatma Sawas mai wannan mage, tare da wasu magunan bakwai da ta ceto rayuwarsu.

A halin yanzu wannan mata mai shekara 24 ba ta da aikin yi amma tana bukatar Dirhami dubu hudu da 500 kafin ta dauki magenta zuwa gida. Kum a kudin maganin yana karuwa ne gwargwadon kwanakin da kyanwar ta kara a asibitin.

Don ta samu ta biya kudin maganin Sawas na ta yin sakar hannu har ma da kayan was an yara. Wadannan kayan wasa farashinsu ya kama a ko’ina daga Dirhami 30 zuwa 200. A halin yanzu ta tara Dirhami 500.

“Mage mai babban ni mna ceceta kuma yau ta yi shekjara shida tare da ni. Ita ce jaririyata kuma tana cikin iyalaina. Zan yi duk abin da zan  iya yi don  ganin ta samu saukin cutar da ke damunta,” inji Sawas.

Wannan Balarabiya ta fara aikin sakar ne shekara biyu da suka gabata, in data rika yin kayan jarirai, wadanda suka hada da barguna da matasan kai da malfa da takalma da jakunkuna. “Ina kuma yin kaya na musmaman gwargwadon bukatar da mutane suka gabatar mini,” a cewarta.

Ta yi nuni da cewa tana rainon maguna a duk sa’adda ta samu dama, tunda tana da kyakkyawan wajen killace su. “Muna cikin wata irin duniya da muka mayar da hankali kacokam kan mutane, amma mun manta da kyautata walwala da jin dadin  dabbobi. A matsayinmu na mutane, kamata ya yi a ce muna kula da sauran dabbobi tunda su ma wani bangare ne na al’umma da rayuwa,” inji Sawas, inda ta yi nuni da cewa nuna irin  wannan kulawar ba karamin al’amari ba ne.