Da Dumi Dumi

Balotelli ya sai wa budurwar da zai aura zoben Naira miliyan 250

Budurwar shahararren dan kwallon Italiya da yanzu haka yake wasa a kulob din AC Milan, Mario Balotelli, mai suna Fanny Negensha a shekaranjiya Laraba ta fito karara ta tabbatar wa duniya cewa saurayinta  Mario ya sai mata zobe mai hade da  sarka da kudinsu ya kai Fam dubu 100 kwatankwacin Naira miliyan 250 a matsayin baiko.
Budurwar wacce ta tabbatar da haka a kafar sadarwarta ta nuna hoton zoben da sarkar da ta yi ado da su don tabbatar da ikirarinta.  
Jim kadan da wannan labari ne masoyanta da kuma masoyan dan kwallon suka rika rige-rigen aika mata sakon taya murna da kuma na fatan alheri.
Rahoton ya kara da cewa, Balotilli mai kimanin shekara 22 da haihuwa tuni ya yanke shawarar auren budurwar tasa ’yar asalin kasar Beljiyam saboda irin soyayyar da ke tsakaninsu, asalima an nuna bai taba yin soyayya da wata budurwa kamar yadda ya fada tarkon soyayya da wannan budurwar a wannan lokaci ba.
Sai dai rahoton ya ce ma’auratan ba su fadi takamaiman rana ko watan da za a yi shagalin bikin nasu ba.
Wata majiya kuma ta kalato cewa masoyan sun samu sabani a watan jiya (Mayu) jim kadan bayan da Balotelli ya fada wa manema labarai cewa da kulob din Real Madrid da ke Sifen ya doke na Brussia Dortmund a gasar zakarun kulob na Turai da ya umarci budurwar tasa ta kwana da su.  An ce wannan kalami da dan wasan ya furta bai yi wa budurwar tasa dadi ba da hakan ya janyo sabani a tsakaninsu.  Sai dai an ce tuni suka shirya bayan da dan kwallon ya nemi ta yafe masa a bisa kuskuren da ya yi.