✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bam a coci: Dana Nathaniel bai taba zama  Musulumi ko na kwana daya ba – Mahaifi

Mahaifin matashin da aka kama da wani abu da ake zargin bam ne a wani coci da ke Sabon Tasha a Kaduna, Mista Samuel Ezikiel…

Mahaifin matashin da aka kama da wani abu da ake zargin bam ne a wani coci da ke Sabon Tasha a Kaduna, Mista Samuel Ezikiel ya tabbatar da cewa sunan dansa Nathaniel Samuel kuma mabiyin addinin Kirista ne.

Mahaifin ya kuma bayyana cewa Nathaniel ba ya da wata alaka da sunan Muhammad Sani, kamar yadda wadansu suka rika yadawa a Intanet.

An kama Nathaniel Samuel ne a ranar Lahadin da ta gabata, a lokacin da aka ya shiga cocin Libing Faith da ake kira da Winners Chapel, a Unguwar Sabon Tasha dauke da wani abin da ake zargin bam ne da ake shirin hallaka  jama’a da shi.

Dubunsa ta cika ne lokacin da mutanen da ke zaune kusa da shi a cikin cocin suka lura da jakar da ya ajiye inda ya shiga ban-daki. Kuma bayan sun dauki lokaci ba su ga ya dawo ba sai suka sanar da jami’an tsaro da ke cocin, wadanda suka kama bincike har suka gano matashin a cikin bayi ta amfani da kyamarar tsaro.

Sai dai bayan an kama shi an  mika shi ga ’yan sanda sai labari ya yadu cewa ai matashin wanda ya ce sunansa Nathaniel Samuel kuma mabiyin addinin Kirista ne, sai wadansu suka musanta bayanin da ’yan sanda suka bayar, inda suka ce  wai Musulmi ne mai suna Muhammad Sani.

Ganin haka ne sai ’yan sanda suka sake fito da shi ga manema labarai, inda ya nanata  cewa sunansa Nathaniel ne ba Muhammad ba, kuma ya yi karatun zama Fasto a kwalejin da ke karkashin cocin.

“Sunana Nathaniel Samuel kuma ni ma’aikaci ne a Cocin Libing Faith, Sabo. Na kuma yi karatu a kwalejin da ke karkashin cocin domin zama Fasto. A ranar da na je coci ne sai na ji cikina ya dan murda, kamar zazzabi ya kama ni. Shi ne na ce bari in shiga bayi in yi bayan gida, to ina cikin bayin sai aka zo aka kama ni, wai an ga abubuwan fashewa a cikin jakata,” inji shi.

Ya ce “Ni ban san aikin bam din ba, domin wata yarinya ce ta ba ni a cikin bakar leda kuma ban duba ba, domin tunanina bai zo hakan ba sai daga baya na ga abin da na dauka.”

Kan rade-radin da ake yi game da sunansa ya nanata cewa: “Ni sunana Nathaniel Samuel kuma ni Kirista ne amma rashin sani ne da tsautsayi ya sa ni, idan har zan fada maka gaskiya.”

Aminiya ta ziyarci gidan su matashin a kauyen Marabar Damishi, inda mahaifinsa mai suna Samuel Ezikiel ke zaune.

Mahaifin ya nuna matukar damuwarsa  kan zargin da ake yi wa dansa, inda ya ce matashin yana shaye-shaye.

“Ni dan kabilar Jarawa ne daga Jihar Bauchi kuma Nathaniel dana ne. An  haife shi ne a 1991. Da ya girma sai ya tsinci kansa cikin shan kwaya kuma duk kokarin da na yi in hana shi ya ki jin abin da nake fada masa,” inji mahafin matashin.

Kan ko matashin na zama a gida, sai ya ce “Gaskiya ya dade da barin gida kuma da ya dawo makon jiya. Na tambaye shi me ke damunsa saboda ya dan canja mini, ba yadda na san shi ba. Na fahimci kalamansa ba su kan saiti. Zai fada maka wani abu yanzu, can kuma sai ya fada maka wani abin daban.

“Ya zo ranar Asabar da safe kuma tunda ya fita ban sake ganinsa ba sai kurum a ranar Lahadi na ji abin da aka ce ya aikata. Na ji an ce ’yan sanda sun zo gidan nan amma lokacin ba na nan kuma ba su sake dawowa ba.

“Amma jami’an SSS da ke Chikun sun zo nan kuma na yi musu bayanin abin da na fada maku a yanzu,” inji shi.

Kan yadda ya ji lokacin da labarin dansa ya same shi, ya ce, “Abin da kawai ya dame ni shi ne rayuwar mutanen da ya nemi hallakawa, idan har da gaske ne ya dauki bam. Domin da a ce shi kadai ne ba zan damu ba amma akwai mutane cikin cocin. Wannan abin ne ya dame ni,” inji shi.

Game da ko dan nasa Musulmi ne sai ya ce, “A’a, Kirista ne kuma ba ya da wata dangantaka da Musulmi (ko Musulunci) koda na kwana daya.”  Ya ce sun taba kai shi asibiti a shekarar 2012, a watan Disamba daga bisani aka sallame shi saboda ba ya da halin ci gaba da kulawa da shi.

Da Aminiya ta tambayi Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Jihar Kaduna, Rabaran Joseph Hayab, da wakilinmu ya tarar da shi a gidan mahaifin Nathaniel, kan  wane mataki za su dauka idan ya tabbata cewa Nathaniel bam yake dauke da shi, sai ya ce “Ba mu da wani mataki, hukuma ce ke da mataki. Kamar yadda babansa ya fadi ne, da bam yake dauke da shi da ya kashe mutane da yawa. To, idan bam ne ai mutumin da ya kai bam da nufin kashe mutane, za a hukunta shi idan kuma ba bam ba ne sai ya taimaka domin a kara wayar da kan jama’a. Akwai abin da na lura da shi wanda yake da dan damuwa, wato idan ba bam ba ne kamar yadda ya ce, ka ga ai ba ranar biki ba ce, ballantana ya ce an gayyace shi ne ya je ya saka.”

“In da ma ya tayar da abin yana iya rikitar da mutane, a ji tsoro har ya kai ga an samu turereniya. Ka ga ke nan abubuwan akwai damuwa da yawa ciki amma abin da ya fi shiga zuciyata shi ne, yaya hankalinsa yake?

“Yau maganar kwaya ta yi yawa a Najeriya, ba mu dauki mataki domin magance maganar kwaya ba. Wata rana a kan yara masu shan kwaya za mu yi fada mu kashe juna, daga baya sai mu gane mun yi fada ne a kan ’yan kwaya.”

Kan ko suna kokarin kare wanda ake zargin ne saboda Kirista ne? Sai ya ce, “A’a, haba, ai tun ba mu san wannan maganar ba ma cewa na yi ko dan gidana ne in zai cuci jama’a, a kama shi; ko mahaifina ne idan har zai cuci jama’a a kama shi. Da na zo na ce mu ba za mu yarda namu ya cuci mutane ba.

“Amma kamata ya yi a gane wane ne shi, kuma mene ne damuwarsa, ba wai a sake shi ba. A’a, a san me ke damunsa, domin wannan zai taimaka gwamnati ta dauki mataki. Sai mu yi magana yadda za a gyara ’ya’yanmu da suke lalacewa; domin wadannan fa ba su fahimci addini ba.

“Babu ruwanmu da addininsa ko sunansa, abin da kawai ke gabanmu shi ne wannan babban laifi da ya nemi aikatawa; wanda muke ganin akwai bukatar a duba saboda kauce wa hayaniyar da ke faruwa ya sa muka shiga binciken sanin wane ne shi, Nathaniel ko Muhammed saboda kauce wa  cece-ku-ce ya sa na binciko inda mahaifin yake,” inji shi.

Ya ce “Amma idan an shiga siyasar suna ko addininsa, to akwai dan jahilci a ciki da wauta. Mu yi amfani da wannan darasi domin gyara wadannan kura-kurai, maimakon mayar da siyasa a kan wadanda za su cuce mu. Mugu ba ya da kabila, mugu ba ya da addini, mugu ba ya da bangare, mugu na cutar da mutane ne. Mutane su hada hannu tare a tona asirin mugu.”

Ya ce za su yi addu’a ga matashin, idan ’yan sanda sun kammala bincikensu sun  tabbatar da cewa abin da yake rike da shi ba wanda zai kawo wa mutane damuwa ba ne, idan ya dawo za su nemi hanyar da za a taimaki babansa domin ya taimake shi. “Amma a yi bincike don kada gobe ya zama an rufe abin da ba a sani ba. A Irin halin da yake ciki, mugu na iya ba shi abin da ya zama mugunta ya je ya yi ba mu sani ba. Shi ya sa muke son a yi bincike,” inji shi.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan a Jihar Kaduna, Yakubu Sabo ya ce abubuwan da aka samu cikin jakar matashin a cikin cocin, abubuwa ne da ake zargin na fashewa ne.

“Irin mutane da ke da nufin kirkiro rashin fahimta suna yinsa ne da wata manufa, mu kuma abin da kullum muke son nuna wa jama’a shi ne, shi mai aikata laifi kansa kurum ya sani, babu ruwansa da wata kabila ko addini.

“Laifi bai san addini ko kabila ba, domin babu wata al’ada ko kabila a kasar nan da ta yarda a yi laifi. Ba kuma addinin da ya yarda a yi laifi. Idan mutum ana zarginsa da aikata laifi, a dauke shi a matsayin wanda ake zargi da aikata laifi ba tare da lura da launinsa ba.

“Wannan ya sa muke son a wayar da kan mutane cewa abin da muke yi muna yinsa ne don kasar nan da jama’ar kasar nan,” inji shi.

 

Bayanin asibiti kan Nathaniel Samuel

Da Aminiya ta ziyarci Asibitin masu Tabin Kwakwalwa da ke Kaduna domin tantance kO an taba kai matashin domin yi masa magani kamar yadda mahaifinsa ya bayyana, hukumar asibitin ta ce ba za su iya tabbatar da an taba kawo mai wannan suna ba ko an taba yi masa magani ba.                                                                                                                                                   Shugaban Asibitin, Farfesa Abdulkareem Jika Yusuf ne ya bayyana wa Aminiya hakan a ofishinsa, ya ce doka ba ta ba su damar fitar da bayanan mara lafiya ba sai dai idan kotu ce ko jami’an tsaro a yayin bincikensu suka nemi a ba su bayanan.

Ya ce ba su fitar da bayanan mara lafiya sai da izininsa ko kamar yadda ya ce kotu ta musamman ta ba da umurnin yin hakan, sai su bi umurni. “Ban ji dadin cewa ba zan iya ba ka wannan bayanai da ka zo nema ba sai da izinin mara lafiyan. Saboda haka a yanzu dai ba zan iya cewa ba mara lafiyanmu ba ne, haka kuma ba zan cewa mara lafiyanmu ba ne, har sai sun fito da shaidar cewa mara lafiyanmu ne shi. Sannan shi ko ’yan uwansa su ba mu izinin fitar da bayanansa a rubuce ko kotu ko kuma jami’an tsaro a cikin bincikensu, za mu ba da goyan baya,” inji shi.