✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bamu amince da zaben Kano ba, a sanar da Abba matsayin zababben Gwamna- PDP

Babbar jam`iyyar adawa ta PDP ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC da ta sanar da dan takarar Gwamnan jam’iyyar PDP Abba…

Babbar jam`iyyar adawa ta PDP ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC da ta sanar da dan takarar Gwamnan jam’iyyar PDP Abba K. Yusuf  a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan jihar Kano.

Jam’iyyar PDP ta ce, Abba Yusuf ne ke kan gaba a kurki’un sahihin zaben da aka yi na baya, kuma shi ne keda kuri’un jihar kashi biyu cikin uku.

Sakataren hulda da jama’a na PDP Mista Kola Ologbondiyan ne ya fitar da sanarwar a yau, ya kuma ce a zaben Gwamnan da aka yi yau 23 Maris 2019 babu wata rumfar zabe mai sakamako sahihi Abba Yusuf ne akan gaba da dan takarar Gwamnan APC Abdullalhi Ganduje da kuri’u dubu 26 a zaben baya.