✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bamu da hannu a kisan ‘yar shugaban Afenifere- Fulani Makiyaya

Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyatti Allah ta nesanta kanta game da kisan ‘yar shugaban kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere, Funke Olakunrin, sakataren Kungiyar na Kasa…

Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyatti Allah ta nesanta kanta game da kisan ‘yar shugaban kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere, Funke Olakunrin, sakataren Kungiyar na Kasa Alhaji Usman Baba Ngazarma, ne ya bayyana haka a wata takardar sanarwa da ya rabawa manema labarai a ofishin kungiyar da ke birnin tarayya Abuja.

Ya ce, Fulani makiyaya sun yi Allah wadai da kisan kana abin takaici ne yadda wasu kafafan yada labarai ke alakanta fulani makiyaya da kisan lamarin da wasu masu neman tada zauna tsaye ke amfani da shi wajen cinma manufar su na tada tarzoma inda ya yi kira ga jam’an tsaro da su tabbatar sun kame wadanda suka aikata kisan domin su fuskanci hukumci.