Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Ban aikata laifi lokacin da nake Ministan Abuja ba – Bala Mohammed

Tsohon Ministan Abuja, Bala Mohammed

Dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar PDP, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya ce bai aikata wani laifi ba lokacin da yake Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja.

Sanata Bala Mohammed ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da batun cewa ya kai Hukumar EFCC kara kuma ya yi nasara kan shari’ar. Ya ce “Ni ne na kai kaina da kaina wajen Hukumar EFCC saboda na yi imani cewa komai za a yi, a yi gaskiya da adalci, ina Turai aka shaida mini cewa EFCC na nemana, lokacin da na dawo sai na samu takardar gayyatar da suka yi mini, na dauka gayyata ce irin ta yau da kullum na kai kaina. To amma sai suka tsare ni, na yi iyakacin kokari har suka ba da belina, bayan sun gindaya mini sharuddan beli, kuma na cika dukan sharuddan, amma suka ki sake ni sai da na shafe kwana 45 a hannunsu. Da na ga haka sai tafi kotu, don ni a zatona za su kai ni kotu ce, amma ba su yi haka ba, sai kotun ta ba da umarni a sake ni, ba su sake ni ba har kwana 45. Na samu karin kwana30 a hannunsu bayan umarnin kotu, da na kai su kara kotun ta ba da umurnin a sake ni, amma aka ki, wannan ya sa kotun ba ta ji dadin abin da suka aikata ba, amma a karshe Allah Ya taimake ni na yi nasara a kansu, kotu ta ce su biya ni diyyar Naira miliyan biyar.”

ADVERTISEMENT

Sanasta Bala ya ce ya ji dadin hukuncin da kotun ta yi don wannan ne ya nuna cewa mutum zai iya samun adalci a kasar nan komai girman cin zarafi da za a yi masa, “Kuma dama wuri na karshe da mutum zai je don neman a yi masa adalci ke nan, kuma sashen shari’a sun kasance masu adalci, don sun nuna ba su da gefen da suke fifitawa,” inji shi.

Ya ce wannan hali shi ya ba shi kwarin gwiwar ci gaba da zama cikin kasar nan har ma ya shiga cikin harkokin siyasa, saboda ya san ban aikata wani laifi ba.

ADVERTISEMENT

Kan batun sauran shari’un da ke kansa a gaban kotu kuwa, Sanata Bala ya ce “Ba zan so in sha gaban kotu ba balle in ce uffan a kai, amma kuna sane da tabbacin da EFCC ta bayar na cewa ba wani korafi da aka samu daga Ma’aikatar Babban Birnin Tarayya, Abuja, ko wani mutum ko wasu gungun mutane cewa an sace wasu kudade ko ga wani laifin da na aikata da ya cancanci a bincike ni ba, illa iyaka dai su sun ce suna da wani abu da ake kira  bayanin sirri, to muna jira mu san abin da suke nufi da haka.”

Tsohon Ministan ya ce a shirye yake ya bayar da bayanin dukan abin da suke zarginsa a kai.

Ya ce ya yi imani cewa Allah Yana bayan mai gaskiya kuma yana sa ran da taimakonSa, tunda ya san bai aikata laifin komai ba, illa iyaka ya yi ayyuka na kyautata rayuwar al’ummar da ke zaune a Abuja kuma Allah zai bayyana gaskiyarsa.

Dangane da sanya hannu kan yarjejeniyar zama lafiya da dukan ’yan takarar Gwamna Jihar Bauchi suka yikuwa, Sanata Bala ya ce yunkuri ne mai kyau da zai haifar da zaman lafiya kuma ya ja hankalin jami’an tsaro da hukumar zabe kan su tabbatar da gaskiya da adalci a tsakanin dukan ’yan takara ba tare da nuna fifiko ba.

Sannan ya koka da yadda ’yan sanda suka shiga cikin cire fastocin ’yan takarar jam’iyyun adawa suna barin na masu mulki, ga kuma tsare magoya bayansu da kuma dukan tsiya da jami’an ke yi musu.