✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban ci kudin kowa a PDP ta Jihar Jigawa ba – Salisu Mamuda

Shugaban Jam’iyyar PDP reshen Jihar  Jigawa Alhaji Salisu Mahamuda Kuit ya ce babu wani mutum da zai iya daga ido ya kalle shi ya ce…

Shugaban Jam’iyyar PDP reshen Jihar  Jigawa Alhaji Salisu Mahamuda Kuit ya ce babu wani mutum da zai iya daga ido ya kalle shi ya ce ya ci kudinsa a Jam’iyyar PDP domin ya tsare mutuncinsa da kujerarsa. Kuma alakarsa da kowa tana da kyau a cikin jam’iyyar.

Alhaji Salisu Mahamuda ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Dutse, inda ya ce jita-jitar da ake bazawa cewar jam’iyyar ta ware wasu daga cikin ’ya’yanta ba ta tafiya da su ko zargin sun amshi kudi a wajen wadansu don gudun kada a sauke su daga shugabancin jam iyyar ba gaskiya ba ne, wadansu ne marasa kishi masu son bata sunan jam’iyyar suke kokarin yi wa jam iyyar zagon kasa.

Ya kuma musanta batun cewa jam’iyyar ta ki sayar wa wadansu magoya bayan Malam Aminu Ringim fom din tsayawa takara, su kuma sun je Abuja sun sayo. Ya ce ai dama kofa biyu ce, kowa yana da damar ya saya ko a Dutse ko ya je Abuja ya saya duk daya ne amma batun cewa an ki sayar wa wadansu ba gaskiya ba ne.

Shugaban ya kara da cewa bayanan da suke zagayawa cewa akwai baraka a cikin Jam’iyyar PDP saboda jita-jitar an samu baraka tsakanin tsohon Gwamna Sule Lamido da tsohon dan takara gwamnanta Malam Aminu Ringim ba su san da wata baraka ba.

Da ya juya kan wadanda aka amshi bakuncinsu a jam’iyyar da suka shigo daga Jam’iyyar SDP ya ce sun yi babban kamu, kuma nan gaba kadan ne za a shirya gagarumin taro da za a gayyato manyan baki daga Abuja da shugabannin jiha da na kananan hukumomin jihar da na mazabu a hedikwatar jihar domin karbar wadanda suka dawo jam’iyyar a ba su tikitin shigowa PDP.

Ya ce yanzu haka jam’iyyar ta kafa kwamiti a shiyyoyi uku domin bai wa kowa damar tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar don ganin an samar da shugabannin jam’iyya a matakin jiha da kananan hukumomi da mazabu.