Da Dumi Dumi

Ban ga amfanin ware ranar 12 ga Yuni a matsayin Ranar Dimokaradiyya ba – Atiku

Ban takarar Shugaban Kasa a zaben da ya gabata a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce kamata ya yi ranar 12 ga  Yuni ta kasance ranar jimami da fittatun ’yan gwagwarmayar kare dimokuradiyya za su lalubo yadda kasar nan za ta kai ga cimma nasara, A sanarwar da mataimakinsa na musamman kan harkokin watsa labarai Paul Ibe ya fitar ya ce bai kamata a ce an mai da ranar 12 ga Yuni a matsayin Ranar Dimokuradiyya ba, bayan da gwamnati ta kasa girmama doka da yin watsi da umarnin kotu, da take hakokin dan Adam.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya kara da cewa shi bai ga amfanin ware wannan rana ta zama ranar hutu ba, bayan ga al’ummar kasa ba su da ’yancin samun ingantatciyar rayuwa, inda a yanzu a duniya Najeriya ce hedkwatar talauci. “Domin hakan babu wani amfani a ayyana ranar 12 ga Yuni a matsayin ranar hutu alhali mafi yawan al’ummar kasa ba sa iya samun abin sawa a bakinsu, kuma  kare rayuwarsu ba ya da tabbas, don haka ban ga wani dalili na ware wannan rana ta 12 ga Yuni a matsayin hutu ba, bayan babu ’yancin fadin albarkacin baki, da kuma take shi kansa tsarin dimokuradiyyar. inji Atiku.

 

 

 

ADVERTISEMENT

 

Share